Hu Jintao ya kai ziyara kasar Canada ne bisa gayyatar da babbar gwamnar kasar Michaelle Jean ta yi masa. Yayin da yake ziyara a kasar, Hu Jintao zai gana da shugabannin kasar, ciki har da babbar gwamnar da firaministan kasar, kana zai yi mu'amala tare da mutane daga bangarori daban daban. Kasashen biyu za su daddale yarjeniyoyin hadin gwiwa a fannonin tattalin arziki da kiyaye muhalli da tabbatar da ingancin kayayyaki da al'adu da yawon shakatawa da ba da ilmi da dai sauransu, kuma mai yiwuwa ne za su sanar da matsayin huldar dake tsakaninsu da kuma burin bunkasa dangantakar tattalin arziki da cinikayya a tsakaninsu.(Zainab)