Za a shirya taron shugabanni a karo na 4 na kungiyar G20 a birnin Toronto na kasar Kanada daga ranar 26 zuwa ranar 27 ga wata, inda za a tattauna kan yanayin da duniyarmu ke ciki wajen gudanar da harkokin tattalin arziki, da matsalar cin bashin da kasashen Turai ke fama da ita, da yadda za a samar da wani tsarin ci gaba mai dorewa, da garambawul din da za a yi wa hukumomin hada-hadar kudi na duniya, hade da sa ido kan cinikayyar da ke gudana a tsakanin kasashen duniya da kuma sassan kudi nasu, da dai makamantansu.
Bisa kokarin da gamayyar kasa da kasa suka yi wajen shawo kan rikicin hada-hadar kudi, sannu a hankali an kafa wani tsari na kungiyar G20 da ya kunshi kasashe masu ci gaban masana'antu, da wasu kasashen da ke saurin tasowa a duniya. A watanni 19 da suka gabata, an shirya tarurukan shugabanni na G20 a biranen Washington, da London, da Pittsburgh. Hakan na da alamun cewa, ana kokarin mayar da taron shugabanni na kungiyar G20 ya zama wani tsari na kullum, sa'an nan ya fara canza matsayinsa daga wani dandalin da ake yin amfani da shi wajen fama da rikici zuwa wata hukumar daidaita tattalin arzikin duniya. Sa'an nan, Cui ya bayyana ra'ayin kasar Sin game da muhimmancin kungiyar G20 cewa, 'Taron shugabanni na kungiyar G20 ya zama wani dandali mai muhimmanci da kasashen duniya ke yin amfani da shi wajen tinkarar rikicin hada-hadar kudi, da kuma karfafa hadin gwiwar da ake yi a tsakanin kasashe daban daban'.
A nasa bangren, Zhang Tao, darektan sashi mai kula da harkokin duniya na baitulmalin kasar Sin , ya furta cewa, 'Ta la'akari da yanayin da ake ciki, taron shugabanni na G20 na da ma'ana sosai a fannin karfafa hadin gwiwar kasashen duniya. Ya kamata kasashe daban daban su dauki manufofin da za su tabbatar da karuwar tattalin arzki a kasashen.'(Bello Wang)