An cika shekaru 40 da kulla huldar diplomasiyya a tsakanin Sin da Canada a bana. A lokacin ziyarar Mr. Hu a Canada, kasashen 2 za su daddale takardun hadin gwiwa ta fuskar tattalin arziki da kiyaye muhalli da binciken ingancin kaya da al'adu da yawon shakatawa da tarbiya da dai sauransu. Sa'an nan kuma, ana sa ran cewa, bangarorin 2 za su tabbatar da matsayin dangantakarsu da manufar raya dangantakar tattalin arziki da ciniki.
Har wa yau, za a yi taron koli a karo na 4 na shugabannin kungiyar G20 a ran 26 zuwa 27 ga wata, inda Mr. Hu da sauran shugabannin kungiyar da jami'an kungiyoyin kasa da kasa za su halara. A yayin taron, za a tattauna halin da duniya ke ciki ta fuskar tattalin arziki da matsalar basusuka a Turai da kuma tsarin raya tattalin arziki mai dorewa da daidaituwa da dai sauransu. (Tasallah)