in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi bikin ranar rumfar Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo a yayin bikin EXPO na Shanghai
2010-06-23 16:59:27 cri

Ranar 23 ga wata, rana ce ta rumfar Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo a wajen bikin baje-koli na kasa da kasa na EXPO a birnin Shanghai. Mataimakin babban wakili na gwamnatin kasar Sin kan harkokin bikin EXPO Wang Sifa, da ministan kula da harkokin kasuwanci da kamfanoni kanana da matsakaita Bernard Biando Sango sun halarci bikin ranar rumfar, gami da gabatar da jawabi.

Mista Wang Sifa ya bayyana cewa, a cikin rumfar Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo, ana kokarin nuna abubuwan da suka fi jawo hankalin jama'a da kasar take da su, gami da kyakkyawan fata ga makomar kasar. Mista Wang ya ce, Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo, daddadiyar aminiyar hadin-gwiwar kasar Sin ce, kuma kasar Sin ta godewa Congon saboda cikakken goyon-bayan da take nunawa bikin EXPO na Shanghai.

Har wa yau, a cikin jawabin da ya gabatar, Mista Bernard Biando Sango ya nuna cewa, bikin EXPO na Shanghai ya samar da wani kyakkyawan zarafi ga mahalarta bikin gami da goman miliyoyin masu kallo a fannin kara fahimtar duniya baki daya. Haka kuma ya yi imanin cewa, Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo zata karfafa mu'amala da hadin-gwiwa a tsakanin ta da kasar Sin a fannonin diflomasiyya, da kasuwanci, da al'adu, da kimiyya da fasaha da sauransu.(Murtala)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China