in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan jaridar kasar Austria sun nuna yabo sosai ga bunkasuwar yankunan dake yammacin kasar Sin
2010-06-23 16:05:00 cri
A ranar 23 ga wata, an kawo karshen aikin kai ziyara ga bikin baje koli na duniya na Shanghai na 'yan jaridar kasashen Sin da Austria, wanda gidan rediyon kasar Sin, da kulob din 'yan jarida na kasar Austria ne suka shirya tare. Saurin bunkasuwar yankunan dake yammacin kasar Sin ya ba da kyakkyawar alama a zuciyar 'yan jarida na kasar Autria.

Wannan kungiyar 'yan jarida ta kunshi da mutane 16 daga gidan rediyon kasar Sin da kulob na 'yan jarida na kasar Austria. A lokacin ziyararsu a nan kasar Sin, sun kai ziyara a birane biyar, ciki har da Shanghai, Shaoxing, Hangzhou, Xi'an, Beijing, kazalika sun kai ziyara ga bikin EXPO na Shanghai, da wasu shahararrun masana'antu da wuraren yawon shakatawa, da kuma wasu kafofin watsa labaru, kamar su gidan rediyon kasar Sin CRI, da gidan talibijin Beijing, da sauransu.

Mambobin kulobu na 'yan jarida na kasar Austria sun yi farin ciki sosai saboda sakamakon da suka samu a yayin ziyararsu a kasar Sin. Sun bayyana cewa, wannan ziyarar ta taimake su kwarai wajen kara fahimtar babbar nasarar da kasar Sin ta samu sakamakon manufar yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje, musamman ma saurin bunkasuwar yankunan dake yammacin kasar. Wani daga cikinsu Kasic Wolfgang ya ce,

'Wannan ne karo na 5 da na kawo ziyara a nan kasar Sin, na ga manyan sauye-sauye da kasar ta samu a ko wace ziyara, kasar Sin tana samun bunkasuwa, tana kuma kara taka muhimmiyar rawa a dandalin kasashen duniya. A kan samun wannan saurin bunkasuwa a wasu manyan biranen kasar, ciki har da Beijing, Shanghai, Hongkong, ko wasu biranen dake kusa da teku, amma yanzu ana iya ga alamar bunkasuwar tattalin arziki a yankunan dake yamma da tsakiyar kasar.'

Babban taken bikin EXPO na Shanghai na shekarar 2010 shi ne, 'Birni mai kayatarwa da rayuwa mai inganci'. Bayan da suka kammala ziyara a farfajiyar bikin baje koli na duniya, Kasic ya bayyana cewa, rumfar kasar Sin ta nuna wannan manufa sosai. Ya kara da cewa, birnin Beijing na gudanar da ayyuka yadda ya kamata a fannin bunkasuwarsa, kamar misali, wasu gine-gine na birnin sun kiyaye halin gargajiya, kuma a sa'i daya an shigar da sigar zamani a ciki.

Shugaban kulob din 'yan jarida na kasar Austria, Fred Turnheim ya taba shiga aikin kai ziyara a jihar Tibet na 'yan jaridar kasashen Sin da Austria a shekarar 2007, ya gayawa manema labaru cewa,

'Ziyarar nan da ta shekarar 2007 dukkansu masu ban sha'awa ne, amma duk da haka akwai bambanci a tsakaninsu. Musamman ma a birnin Shanghai, na taba kawo ziyara a Shanghai a shekarar 2007, amma yanzu an samu manyan sauye sauye a cikin shekaru kusan 3 da suka gabata.'

Kan abincin kasar Sin, Turnheim ya ce,

'Ko shakka baku, ina son abinci na birnin Shanghai, lallai ina son dukkan abincin Sinawa.'

Bisa gayyatar da gidan rediyon kasar Sin ya yi masa ne, a ranar 10 ga wata, wakilai 11 daga kulou na 'yan jarida na kasar Austria sun isa birnin Shanghai, don fara ziyararsu a nan kasar Sin.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China