in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar G20 za ta yi kokarin kara yin hadin gwiwa da sauran sassan duniya bayan an warware rikicin hada-hadar kudi na duniya
2010-06-23 15:35:45 cri
Za a gudanar da taron koli na kungiyar G20 daga ranar 26 zuwa 27 ga wata a birnin Toronto na kasar Canada. Yayin da ake ta kokarin shawo kan rikicin hada-hadar kudi na duniya, muhimmiyar rawar da kungiyar G20 take takawa ta jawo hankalin dukkan duniya. An daidaita matsayin kasashe membobin kungiyar a gun taron koli na birnin London da na birnin Pittsburgh, wannan ya ba da taimako wajen farfado da tattalin arzikin duniya. Bayan an samu damar warware rikicin hada-hadar kudi na duniya, ko kungiyar G20 za ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa? Wasu masana sun bad a tabbatacciyar amsa ga wannan tambaya.

A gun tarurrukan koli 2 na kungiyar G20 da aka yi a shekarar 2009, an dora muhimmanci kan rikicin hada-hadar kudi. Bayan da manyan kungiyoyin tattalin arzikin duniya suka yi kokari, an samu kyautatuwa a yanayin tattalin arziki da ake ciki a yanzu. Mataimakin shugaban asusun kula da zaman lafiyar duniya na Carnegie na kasar Amurka Douglas Paal ya bayyana cewa, yanayin da kungiyar G20 ke fuskanta ya sha bamban da na bara, sabo da haka, an samu canji kan abubuwan da za a tattauna a gun taron koli na birnin Toronto. Mr Paal ya ce:"Yayin da ake kokarin shawo kan rikicin hada-hadar kudi na duniya, an tsara burin daidaita tattalin arzikin duniya a gun taron koli na kungiyar G20, sabo da haka, mun shiga wani yanayi da ya bambanta da na da. Misali, kasar Sin ta riga ta samu nasara wajen gyara tsarin tattalin arziki. Don haka, ya kamata mu tabbatar da nasarar da aka samu a gun taron koli na birnin Toronto. Ba shakka, za a tattauna kan batutuwa game da yankuna masu amfani da kudin Euro domin matsalar yawaitar bashi da ta abku a kasar Girka."

Bisa rahotanni da aka bayar, an ce, ana ta kokarin farfado da tattalin arzikin duniya. Direktan sashen kula da hadin gwiwa a duniya na jami'ar New York ta kasar Amurka Bruce Jones ya bayyana cewa, ko da yake tattalin arzikin duniya ya na samun bunkasuwa cikin sauri, kungiyar G20 ta iya ci gaba da sa kaimi ga hadin gwiwarsu. Mr Jones ya ce:"Muna iya ci gaba da yin hadin gwiwa a fannoni daban daban, kamar hada-hadar kudi da kiyaye zaman lafiya da yaki da 'yan fashin tekun Somaliya da kuma cinikayya. A takaice dai, ana iya yin hadin gwiwa a dukkan fannoni."

Mr Jones ya kara da cewa, a halin da ake ciki a duniya, babu wata kasa ko wata kungiya da za ta iya warware matsaloli da kanta. Sabo da haka, bunkasuwar kungiyar G20 da ta kunshi kasashe masu arzikin masana'antu da sabbin kasashen da suka fi samun ci gaban tattalin arziki ta zama muhimmin matsayi.

Amma Mr Paal ya nuna cewa, a matsayin wani dandalin tattaunawa, kungiyar G20 tana cikin matakin farko wajen samun bunkasuwa.

Game da wannan, Mr Jones ya yi hasashe da cewa, ko da yake kungiyar G20 tana da babbar damar samun bunkasuwa a nan gaba, amma ba za ta iya maye gurbin kungiyar G8 a matsayin dandalin tattaunawa na duniya daya kacal ba. Amma bayan wasu shekaru, mai yiwuwa ne yanayi zai canja. Mr Jones ya ce: "A ganina, wannan ya bayyana cewa, yanayin duniya yana canjawa. Sabo da haka, kungiyar G8 za ta ci gaba da kokarin warware matsalolin da kungiyar G20 ba ta iya warware ba. Amma ina tsammani cewa, wannan wani aikin wucin gadi ne, a shekaru 2 zuwa 3 masu zuwa, kungiyar G20 za ta maye gurbin kungiyar G8."

Ban da wannan, Mr Jones ya bayyana cewa, yanzu dai an riga an kafa tsarin kungiyar G20, a nan gaba kuma kungiyar G20 za ta kara daukar alhaki mai muhimmanci yayin da take yin kira don samun hadin gwiwa a duniya.

Masana da dama sun furta cewa, dalilin da ya sa kungiyar G20 take da damar samun bunkasuwa shi ne shigar sabbin kasashen da suka fi samun ci gaban tattalin arziki, ciki har da kasar Sin, ta taimaka wajen karfafa wakilcin kungiyar G20. Ga kungiyar G20, bunkasuwar sabbin kasashen da suka fi samun ci gaban tattalin arziki tana da babbar ma'ana.(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China