in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bayani kan kaddarar dake tsakanin kasar Faransa da bikin EXPO
2010-06-22 15:01:52 cri
Ranar 21 ga wata rana ce ta rumfar kasar Faransa a bikin EXPO na Shanghai. Idan aka kwatanta da sauran ranakun rumfunan kasashe daban daban, ranar rumfar kasar Faransa ta fi bai wa mutane sha'awa sabo da kaddarar dake tsakanin kasar Faransa da bikin EXPO ta shakaru fiye da dari.

Tun daga shekarar 1855 zuwa ta 1937, an yi bikin EXPO a birnin Paris sau 7, sabo da haka, birnin Paris ya zama birnin da ya fi samun damar saukar bikin a nahiyar Turai. Kowane daga cikin bikin EXPO da aka yi a birnin Paris ya kan burge mutanen kasa da kasa, inda aka gabatar da kayayyakin tarihi masu daraja da yawa da kuma muhimman kayayyakin da aka kirkiro wadanda kuma suka yi babban tasiri ga zaman rayuwar jama'a.

Yanzu, mazauna birnin Paris sun fi son yin amfani da jiragen dake tafiya a karkashin kasa, amma an fara gina hanyoyin jiragen dake tafiya a karkashin kasa na birnin Paris a sakamakon bikin EXPO na shekarar 1900. A tsakiya da kuma karshen karni na 19 da ya gabata, yanayin zirga-zirga ya gamu da cikas, bikin EXPO na shekarar 1900 ya matsa lamba ga gwamnatin birnin Paris sosai, motocin da birnin Paris yake da su ba su iya biyan bukatun masu yawon shakatawa a yayin bikin EXPO ba. Shi ya sa, an fara gina hanyar jirgin dake tafiya a karkashin kasa ta farko ta birnin a watan Oktoba na shekarar 1898. Wannan hanyar jirgin dake tafiya a karkashin kasa ta hada da unguwanni daban daban na farfajiyar bikin EXPO.

Haka kuma, bikin EXPO na Shanghai shi ma ya sanya birnin Shanghai da ya kyautata tsarin hanyoyin jirgin dake tafiya a karkashin kasa, bisa kokarin da gwamnatin birnin Shanghai ta yi, an kammala aikin gina tsarin zirga-zirga na kasa da na ruwa. Hakan ya kawo moriya ga masu yawon shakatawa da suka je birnin Shanghai domin halartar bikin EXPO, kana zai samar da kyakkyawan yanayin zirga-zirga ga mazauna birnin Shanghai a nan gaba.

Bugu da kari, gine-gine da yawa dake birnin Paris suna da nasaba da bikin EXPO. A matsayin daya daga cikin muhimman gine-gine na birnin Paris, hasumiyar Eiffel tana da nasaba sosai da bikin EXPO na shekarar 1889.

Shekarar 1889 ta kasance ta cika shekaru 100 da cimma nasarar babban juyin juya hali na kasar Faransa, gwamnatin kasar Faransa ta yanke shawarar neman samun wani ginin da ka iya bayyana karfin kasar. A karshe dai, an zabi hasumiyar Eiffel da aka gina ta hanyar yin amfani da karfe. A yayin bikin EXPO na shekarar 1889, masu yawon shakatawa kimanin miliyan 2 sun hau kan wannan hasumiya. A cikin shakaru fiye da dari da suka gabata, hasumiyar Eiffel tana gabar kogin Seine, ita ce kuma take shaida ci gaba da birnin Paris ya samu.

Dadin dadawa, a bikin EXPO na shekarar 1900, an nuna sinima ta hanyar yin amfani da na'urar nuna sinima ta hannu. Ko da yake wannan na'ura tana da kara sosai, amma 'yan kallo sun nuna sha'awa ga wannan sabuwar na'ura. A sa'i daya, an gabatar da na'urar da ta iya nuna jerin hotuna daya bayan daya cikin sauri da kuma fim, wadanda suka kasance asalin injin nuna sinima. Ban da haka kuma, a gun wannan bikin EXPO, an gabatar da injin daukan sauti da Edison ya kirkiro, wanda ya aza harsashi ga bunkasuwar sinima. Daga bisani, a cikin wasu shekaru bayan da aka kammala bikin EXPO, sana'ar nuna sinima ta kasar Faransa ta samu bunkasuwa cikin sauri.

A karshe dai, an gabatar da giya mai launin ja a karo na farko a gun bikin EXPO na shekarar 1855. Bayan haka, irin wannan giya ta kara samun karbuwa a duk duniya.

Bikin EXPO ya gaji kyawawan kayayyaki, kuma ya ingiza bunkasuwarsu. Ta hanyar waiwayar bikin EXPO da aka yi kafin shekaru dari a birnin Paris, bikin ya hada birnin Paris da duniya, yanzu, wajibi ne, al'ummar kasa da kasa ta tuna da kayayyakin kasar Sin a gun bikin EXPO na Shanghai.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China