in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Birnin Beijing ya shiga lokacin jin dadin gasar FIFA ta shekarar 2010
2010-06-22 14:02:34 cri
Ibrahim: A ran 11 ga wata, an kaddamar da gasar wasannin kwallon kafa ta cin kofin duniya ta shekarar 2010 a kasar Afirka ta kudu. Sakamakon haka, bayan shekaru 4 da suka gabata, masu sha'awar kwallon kafa a duniya suna murnar sake kallon wannan gasar kamar yadda suke fata. A nan birnin Beijing ma, ko a cikin gine-gine, ko a kan tituna, mutane suna tattaunawa kan batun gasar wasannin kwallon kafa ta cin kofin duniya. Ko da yake akwai nisa sosai a tsakanin kasar Sin da kasar Afirka ta kudu, amma gasar cin kofin duniya tana girgiza mutanen birnin Beijing tamkar yadda ake yin wannan gasa a nan kasar Sin.

Sanusi: A kan hada giya da kwallon kafa. Lokacin da masu sha'awar kwallon kafa suke kallon gasa, su kan sha giya. A zuciyarsu, wannan zaman rayuwa ne mai dadi. A kwanan baya, wato lokacin da aka kaddamar da gasar cin kofin duniya ta kwallon kafa a kasar Afirka ta kudu, an kuma soma bikin shan giya domin jin dadin kallon gasar a wani filin shan iska da ke kusa da rediyo CRI tun daga ran 11 zuwa ran 28 ga watan Yuni. Bugu da kari, za a shirya bukukuwa iri iri a gun wannan bikin shan giya. Mr. Yu Dezhi wanda ke kula da wannan biki ya ce, "A kowace rana muna shirya wani kacici kacici game da gasar cin kofin duniya. Duk wanda ya yi nasara, zai iya samun kyautar da ke da alamar gasar cin kofin duniya. Sannan ana yin gasar shan giya a kowace rana, wanda ya samu nasara, za mu ba shi kyauta, wato kwalbar giyan 'Bishofshof' ta kasar Jamus."

Ibrahim: Bugu da kari, Mr. Yu Dezhi ya ce, an samar da manyan akwatunan talibijin guda 3 da ke hade da wani akwatin talibijin da fadin fuskarsa ya kai murabba'in mita 54, fadin sauran akwatunan talibijin guda biyun ya kai murabba'in mita 35. Sakamakon haka, masu sha'awar kwallon kafa za su iya jin dadin kallon gasar. Mr. Yu ya kara da cewa, "Jimillar fadin wadannan akwatunan talibijin uku ta kai murabba'in mita 120. Sabo da haka, ana jin dadin kallon gasar, kuma muna bude kofar shiga wannan biki har zuwa karfe 12 na dare a kowace rana, wato za a kalli gasa ta biyu da a kan yi a kowace rana."

Sanusi: A yayin da ake shiga lokacin zafi a nan birnin Beijing, idan akwai giya mai sanyi lokacin da ake kallon gasar kwallon kafa, wannan ne yanayin da masu sha'awar kwallon kafa suke so. Sabo da haka, wasu kamfanoni manya ko kanana suke soma gudanar da harkokin kasuwanci lokacin da ake yin gasar cin kofin duniya. Alal misali, a ran 9 ga wata, an soma bikin shan giya na yakar zafi a karo na biyu a unguwar Chaoyang ta birnin Beijing. Madam Gao, wata ma'aikaciyar wani kamfani mai suna "tashar ruwa mai launin shudi" ta bayyana cewa, "Za mu iya kallon gasar cin kofin duniya a lokacin da muke shirya bikin shan giya mai sanyi. Sannan za mu shirya wasu gasanni, kamar gasar shan giya da rera wakoki da kide-kide da dai sauransu."

Ibrahim: A lokacin da ake shiga shekarar yin gasar cin kofin duniya ta kwallon kafa, a kan samu damar sayar da kayayyakin kwallon kafa da yawa. Kafin a soma gasar cin kofin duniya a kasar Afirka ta kudu, ko kamfanin Adidas, ko sauran kamfanonin samar da kayayyakin da suke da nasaba da wasan kwallon kafa, kamar su kamfanin Nike da na Puma da dai makamatansu sun samar da riguna da takalma na wasan kwallon kafa da tutocin kasashen da suka samu damar halartar wannan gasar cin kofin duniya da kofi da mutum-mutumin mashahuran 'yan wasan kwallon kafa. Farashin irin wadannan kayayyaki ya kama daga yuan daya zuwa dubban yuan. A wani kantin sayar da kayayyakin wasannin motsa jiki, yaron kantin ya gaya wa wakilinmu cewa, "Lokacin da ake yin gasar cin kofin duniya, tabbas ne mutane masu sha'awar kwallon kafa za su taru a wani wuri, kuma za su sha giya domin jin dadin kallon wasannin. Kuma tabbas ne suna bukatar wasu kayayyakin wasan kwallon kafa, kamar irin wadannan rigunan da mutane da yawa suke saya kaya ne da masu sha'awar kwallon kafa suke bukata."

Sanusi: Ba ma kawai yawan kayayyakin da suke da nasaba da wasan kwallon kafa da ake sayarwa ya karu cikin sauri ba, har ma yawan akwatunan talibijin da aka sayar a cikin wata daya da ya gabata ya karu sosai. Wani sabis ya bayyana cewa, "A da, bayan ranar 1 ga watan Mayu, ba mu iya sayar da akwatunan talibijin da yawa ba. Amma a shekarar da muke ciki, muna sayar da su kamar yadda muke fata, musamman jama'a sun fi son sayen manyan akwatunan talibijin, wato yawansu da aka sayar ya karu fiye da kashi 50 cikin dari."  (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China