Ta hotuna da fina-finai ne hukumar kula da harkokin 'yan gudun hijira ta MDD ta bayyana irin wahalhalun da 'yan gudun hijira suke fuskanta ta fannonin zaman rayuwa da kuma aiki, kuma ta yi kira da a nuna kulawa ga 'yan gudun hijira da ke cikin birane. A ranar, hukumar ta kuma nada Yao Chen, 'yar wasan kwaikwayo ta kasar Sin, a matsayin wakiliyarta a kasar Sin. Madam Yao Chen, wadda ba da jimawa ba ta kai ziyara ga 'yan gudun hijira na kasar the Philippines, ta ce, ba ma kawai kayayyakin agaji ne 'yan gudun hijira ke bukata ba, a'a, abin da suka fi bukata shi ne damar samun mutumci da amincewa da kuma karbuwa a birane.(Lubabatu)