Kasar Denmark da samu nasara a kan Kamaru da ci biyu da daya. Ko da yake kasar Kamaru ce ta fara samun nasara a wannan wasa a lokacin da shahararren dan wasanta Samuel Eto ya jefa kwallo a ragar Denmark. Amma daga baya kasar Denmark ta rama, sannan kuma ta sake kara wata. Ta haka kasar Kamaru da ta sha kashi har sau 2 ta zamanto ta farko da za ta bar gasar cin kofin duniya a wannan karo.
Har wa yau kuma, kasar Holand ta yi nasara a kan Japan da ci daya mai ban haushi, ta haka bisa nasarar da ta samu har sau biyu, ta zama ta farko da ta fita daga rukuni-rukuni a gasar cin kofin duniya.
Ban da wannan kuma, kasashen Austrliya da Ghana sun yi kunnen doki da ci daya da daya a karawa ta karshe a rukunin D na gasar cin kofin duniya.(Tasallah)