in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban lambun shan iska na gudun zafi na Chengde
2010-06-20 18:39:02 cri
Babban lambun shan iska na gudun zafi da ke birnin Chengde na lardin Hebei a arewa da birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin, lambu ne mai tsawon tarihin shekaru dari 2 ko fiye da sarakuna suka gina. An ce, yau shekaru kusan dari 3 da suka wuce, a ko wace ranar 5 ga watan Mayu bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, sarakunan zamanin daular Qing kan je wannan babban lambun shan iska wato Bi Shu Shan Zhuang a bakin Sinawa, sa'an nan, su kan koma fadar sarakuna, wato Forbidden City da ke birnin Beijing a ranar 9 ga watan Satumba a ko wace shekara. Ta haka, a kan kira babban lambun Bi Shu Shan Zhuang da sunan "fadar bari", wato fadar Ligong, wadda ma'anarta ita ce wurin da sarki kan zama bayan da ya bar fadarsa.

An fara gina babban lambun Bi Shu Shan Zhuang da ke birnin Chengde a shekarar 1730, kuma an yi shekaru 89 ana gina shi. Shi ne lambun sarakuna mafi girma a duk duniya da ake adana shi yadda ya kamata a halin yanzu. Fadinsa ya kai murabba'in mita miliyan 5 da dubu 640, wato girmansa ya ninka sau biyu bisa na fadar Yiheyuan wato Summar Palace da ke birnin Beijing. Chen Jing, mai yi wa maziyarta bayani ta gaya mana cewa,"Akwai wani filin farauta mai suna Mulan da aka kebe domin sarakuna kawai. Sarki Kangxi ya darajanta filin farauta na Mulan sosai, ta haka ya kan yi farauta da yin faratis ta fuskar aikin soja a wajen a ko wace shekara tare da mutane a kalla dubu 17 ko dubu 18, a wasu lokatu, yawan wadanda ke binsa ya kai dubu 70 zuwa dubu 80. Da zummar samar wa wadannan dimbin mutane isassun abinci da wuraren kwana da sauran abubuwan da suka wajaba da kuma biyan bukatun sarakuna don gudanar da ayyukansu, an gina wannan babban lambun shan iska a wurin da ke tsakanin birnin Beijing da filin farauta na Mulan."

Dalili na daban da ya sa aka gina shi ne domin akwai wani sashen Babbar Ganuwa wato Great Wall a tsakanin biranen Beijing da Chengde. A zamanin da, wasu shugabannin kananan kabilun da suka fito daga jihohin Mongolia da Tibet da Xinjiang su kan jira domin samun damar gai da sarakunan zamanin daular Qing a waje da Babbar Ganuwa. Ta haka sarki Kangxi ya gina wannan babban lambun shan iska, kuma ya kan yi rabin shekara yana zaune a wajen a ko wace shekara domin gai da wadannan shugabannin 'yan kananan kabilu. Ta haka sarakunan zamanin daular Qing suka hada kan 'yan kabilun Mongolia da Tibet da sauran kananan kabilu da ke zaune a karkarar bakin iyakar kasa.

A cikin babban lambun shan iska na Bi Shu Shan Zhuang da ke birnin Chengde, bayan an ratsa ta kofar Lizheng da ta Waiwu, an isa wurin da sarakunan zamanin daular Qing su kan gudanar da aikinsu da yin zaman yau da kullum, kuma a kan shirya bukukuwa da shagulgula. Yanzu an mayar da wannan wuri zuwa dakin nune-nunen abubuwan gargajiya, inda ake ajiye abubuwan da sarakuna suka taba yin amfani da su a zamanin da.

Masu karatu, bayan shiga wannan dakin nune-nunen abubuwan gargajiya, da farko kuna iya ganin babban zauren Danpo Jingcheng mai kyan gani. A tsakiyar babban zauren, akwai wata kujerar sarki da aka kera da icen red sandalwood. A kewayen kujerar, ana ajiye wasu kyawawan abubuwan sassaka, wadanda a ganin Sinawa, abubuwa ne na nuna fatan alheri. A bayan kujerar, akwai wata kariya irin ta musamman da aka kera da icen red sandalwood. An saka hotunan mutane 163 da ke noma da gudanar da sauran ayyukan gona a kan kariyar, dukkansu sun yi kama da yadda suke da rai. Hakan ya nuna cewa, a zamanin daular Qing, sarakuna sun mai da hankali sosai kan aikin gona.

Madam Chen ta yi karin bayani da cewa,"An gina wannan babban zaure da icen Nanmu mai daraja sosai duka. An yi amfani da azurfa kilogiram dubu 3 da dari 6 da 50 wato kudin Sin yuan miliyan 14 da dubu dari 6 wajen gina shi, kuma an yi amfani da azurfa kilogiram 600 wato yuan miliyan 2 da dubu dari 4 wajen yin jigilar icen Nanmu. Yanzu ba a iya samun irin wannan icen Nanmu ba. A da, an taba samun irin wannan ice mai daraja a kunkurmin daji a lardunan Yunnan da Guizhou da Taiwan. Icen Nanmu ya yi girma cikin dogon lokaci, ta haka darajar ko wane inch na icen Nanmu ta yi daidai da ta ko wane inch na zinariya. Kusan dukkan manyan kusoshin da muka gani a yanzu, an sarrafa su da icen Nanmu mai tarihin fiye da dubu daya, sa'an nan kuma, ba safai a kan samu icen Nanmu mai kwari. Shi ya sa wannan babban zaure yake da daraja matuka."

A hagu da dama na babban zauren, akwai wani kabad da aka sarrafa da icen red sandalwood, kuma aka sassaka abubuwa a kansa. Tsayinsa ya kai mita 4, fadinsa ya kai mita 2.4, an harhada shi da kananan gutsurori na icen red sandalwood. A fuskar kabad din, an sassaka zane-zane masu kyan gani. Ba a iya ganin irin wannan kabad a sauran wurare ba, sai a babban lambun shan iska na Bi Shu Shan Zhuang kawai.

Ko da yake akwai kayayyakin tarihi masu daraja da yawa a babban lambun shan iska na Bi Shu Shan Zhuang na Chengde, amma yanzu wannnan lambun sarakuna ya kasance wurin nishadi ga dukkan mazauna birnin Chengdu.

A ko wace rana da safe, Gao Deyin, wata tsohuwa ta kan motsa jiki tare da abokanta a babban lambun shan iska na Bi Shu Shan Zhuang na Chengde saboda yana da kyan gani sosai, haka kuma, iska na da ni'ima kwarai. Madam Gao ta ce,"Mu mazauna birnin Chengde mu kan motsa jiki da yin yawo a nan. Wasu kuma su kan yi yawo da dare. Birnin Chengde, wani karamin birni ne da aka gina a babban tsauni. Mazauna wurin suna zaune a kusa da wannan babban gida, ta haka su kan je wajen."

A babban lambun shan iska na Bi Shu Shan Zhuang da ke birnin Chengde, a kan sadu da maziyarta daga sassa daban daban na duniya. Chen Nini, wata budurwa ce da ta kai ziyara a wannan babban lambun shan iska na Bi Shu Shan Zhuang tare da wasu maziyarta daga kasar Malaysia. Ta gaya mana cewa, babban lambun shan iska na Bi Shu Shan Zhuang na Chengde wuri ne da kada a manta da kai masa ziyara, inda ta ce,"Ta fuskar al'adu, na fi sha'awar babban lambun shan iska na Bi Shu Shan Zhuang na Chengde, saboda yana da dogon tarihi. In mun yi ziyara a nan, za mu iya kara sani kan zaman rayuwar sarakuna a zamanin da. Ya fi kyau a yi masa ziyara. A wannan karo, mun yi yini daya kawai muna yin ziyara a birnin Chengde, yau za mu koma birnin Beijing, ba mu da isasshen lokaci, amma zan sake yin yawo a babban lambun shan iska nan, ina so in sake yin ziyara a tsanake a wajen. Kafin zuwanmu a wannan karo, ban dudduba abubuwan da ke shafar wannan babban lambun shan iska ba, ban san shi sosai ba, kuma mun yi hanzari a yayin da muke yin ziyara a nan. Shi ya sa nan gaba in na yi ziyara a nan, zan yi yawo a wajen a tsanake sannu a hankali."(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China