in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yin ziyara a wurin shakatawa na Huayuankou a gabar Rawayen Kogi tare da kara sani kan tarihi
2010-06-20 18:39:02 cri
A ganin al'ummar Sin, Rawayen Kogi wato Huanghe kogi ne da ke renonsu kamar yadda mahaifiya take renon 'ya'yanta. Wasu kan ce, Rawayen Kogi ya samar wa yankin tsakiyar kasar Sin abubuwa mafi kyau, amma a ganin mazauna lardin Henan da ke yankin tsakiyar kasar Sin, Rawayen Kogi ya bai wa garinsu wahalhalu mafi tsanani. A wasu lokuta, kogin ya samar da amfani gare su, amma a wasu lokuta, ya haddasa bala'u. Rawayen Kogi na renonsu, amma watakila ya kwace rayukansu. Kauyen Huayuankou da ke gabar Rawayen Kogi ya sha gamuwa da ambaliyar ruwa da wannan kogi ya kawo masa a tarihi. Amma a duk lokacin bayan bala'in, kullum a kan farfado da kauyen, an maido da kyan surarsa. Yau bari mu je wurin shakatawa na Huayuankou da ke gabar Rawayen Kogi.

An ce, yau shekaru dari 5 ko fiye da haka da suka wuce, wato a zamanin daular Ming ta kasar Sin, wani babban jami'i ya gina wani lambu mai fadin murabba'in kusan kadada 40 a gabar Rawayen Kogi, inda ya noma furanni da itatuwa, wadanda suka fid da furanni a duk tsawon shekara. Mazauna wurin sun yi Alla-alla wajen yin yawo a wajen. Amma a sakamakon sauyawar hanyar Rawayen Kogi, ruwa ya mamaye wannan kyakkyawan lambu, ta haka wannan wuri ya zama wata kwata a kudancin gabar Rawayen Kogi. Mazauna wurin kan kira shi "Huayuankou".

Yanzu ba a tabbatar da cewa, ko wannan lambu na da kyan gani ko a'a a wancan lokaci, amma a hakika dai, akwai dimbin itatuwa da furanni a wurin shakatawa na Huayuankou. Madatsar ruwa ta Jiangjunba na daya daga cikin ni'imtattun wurare a wannan wurin shakatawa. Yu Hanqing, mataimakin darektan kamfanin raya yawon shakatawa na Rawayen Kogi ya yi karin bayani da cewa,"Wani janar wato Jiangjun a bakin Sinawa mai kula da harkokin kogi ya sha samun babban yabo daga mahukunta saboda samun nasarar kula da harkokin kogi. Na baya da shi sun gina wani gidan ibada wato Jiangjunmiao domin tunawa da shi a shekarar 1754. Wannan madatsar ruwa na dab da gidan ibadan, ta haka an nada shi sunanta 'Jiangjunba'."

A cikin gidan ibada na Jiangjunmiao, an nuna girmama ga mala'iku 64 da suka yi kaka gida a Rawayen Kogi a cikin almara. An samu asalin wadannan mala'iku ne daga jami'an kula da koguna na zamanin dauloli daban daban a tarihin kasar Sin. Wadannan mutane sun yi aiki tukuru, sun sadaukar da duk rayukansu kan yaki da ambaliyar ruwa. Ta haka bayan sun rasu, fararen hula ba su manta da su ba, sannu a hankali, sun zama mala'iku a zukatun mutane.

Masu karatu, in kun yi yawo a wurin shakatawa na Huayuankou da ke gabar Rawayen Kogi, ya fi kyau ku kara sani kan wakokin Haozi da masu ja kwale-kwale cikin Rawayen Kogi ke rera domin karfafa hadin gwiwarsu a lokacin aiki. Wakokin Haozi na daya daga cikin muhimman bangarorin al'adun Rawayen Kogi. Wadanda ke zaune a gabar Rawayen Kogi sun fito da su ne a lokacin da suke cin gajiyar kogin tare da yaki da ambaliyar ruwa da kogin kan kawo musu a zamanin dauloli daban daban a tarihin kasar Sin. Zuriyoyin masu jan kwale-kwale sun dade suna zaune a gabar Rawayen Kogi, sun san wannan kogi matuka, haka kuma, sun san kwale-kwale sosai. A lokacin da suke yin gwagwarmaya da igiyar ruwa da babban iska a Rawayen Kogi, sun samar da wakoki masu ban sha'awa kuma masu sigar musamman. A sakamakon sauyawar hanyar kogin, masu jan kwale-kwale kan rera wakokin Haozi na saloli iri iri. A wasu lokuta, su kan rera waka cikin sauri, a wasu lokuta kuma, su kan rera sannu a hankali.

Yanzu rera wakokin Haozi ya kasance shahararren wasan fasaha ne da ake nunawa maziyarta a wurin shakatawa na Huayuankou. A ko wace rana, maziyarta kan ji dadin saurara.

Yanzu a yankin Huayuankou babu kwatar jiragen ruwa, amma wadanda ke zaune a gabar Rawayen Kogi sun samar da wata harkar nishadi, inda mutane kan kara fahimta kan zaman rayuwar masu kama kifi. Ga shi Mr. Xu, wani mai kama kifi, ya yi gyare-gyare kan gidansa zuwa wurin da ke samar wa maziyarta damar fahimtar zaman rayuwar masu kama kifi. Inda ya ce,"Fararen hula da ke zaune a bakin Rawayen Kogi sun samu wadata, masu kama kifi su ma sun samu kudi da yawa. A hakika, Rawayen Kogi kogi ne da ke renon wadanda ke zaune a gabobinsa. Mun ci gajiyarsa sosai. Rawayen Kogi ya yi kama da mahaifiyarmu."

A gabobin Rawayen Kogi, akwai dimbin filaye masu danshi a sakamakon kasancewar kogin. An raya da yawa daga cikin wadannan filaye masu danshi zuwa lambunan halittu na aikin gona da maziyarta, musammam ma wadanda ke zaune a birane suka iya yin yawo. Lambun halittu na aikin gona na Fujing na daya daga cikin irin wadannan lambunan halittu masu ban sha'awa.

An gina lambun halittu na aikin gona na Fujing da ke ratsawa cikin gabobin Rawayen Kogi na kudu da na arewa, tsawonsa ya kai kilomita 8 a gabobin biyu na kogin. In an kwatanta shi da sauran lambunan halittu na aikin gona, wannan lambun halittu na Fujing ya kafu ne a sakamakon jarin da kamfanin Fujing na Taiwan ya zuba shi kadai. Dukkan ma'aikatan kamfanin su ne suka fito daga iyalin Mr. Lian. Mazauna wurin kan kira Mr. Lian da ya kafa kamfanin da sunan "Lao Lian" saboda suna sonsa kwarai. Ya je yankin tsakiyar kasar Sin tare da abinci mai dadin dandano da harkokin nishadi na Taiwan.

Dan wansa ya yi karin bayani da cewa,"Kawuna ya zuba jari kan kafa wannan lambun halittu. Mu mazauna Taiwan dukkanmu muna ganin cewa, Rawayen Kogi na renon mu al'ummar Sin dukka, kamar yadda mahaifiyarmu ta yi. Ta haka muna kokarin ba da gudummawa a gabobin Rawayen Kogi."

A sakamakon kishin gari da kuma kasa matuka, Lao Lian ya haka wani babban tabki mai fadin kadada 40 a cikin lambun halittu na aikin gona na Fujing, ya kuma ba wannan tabki sunan "Riyuehu", wato tabkin "Rana da wata" ke nan. A bakin tabkin an dasa itatuwa bisa layuka 2 domin kiyaye bakin tabkin. Sa'an nan kuma, ana kiwon kifaye misalin dubu 500 da aka samu a Rawayen Kogi kawai a tabkin. Wadannan kifaye suna rayuwa a tabkin ba tare da kulawar da mutane suke nuna musu fiye da kima ba. Haka zalika, filin yin fatsa da filin rairayi na ninkaya da aka samu a lambun halittu na aikin gona na Fujing su ma sun kasance wuraren da ke dacewa da mutane wajen hutawa da yi yawo.

Yanzu in mutane sun yi ziyara a wurin shakatawa na Huayuankou, sun iya waiwayar abubuwan da suka faru a tarihin kasar Sin, haka kuma, sun iya jin dadin kallon ni'imtattun wurare da aka gina ba tare da gurbata muhalli ba a zamanin yau. Wurin shakatawa na Huayuankou wuri ne mai dacewa a fannonin yin ziyara a wurare masu ni'ima da kuma kara sani kan tarihi.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China