Birnin Guiyang, shahararren birnin kasar Sin ne da ya yi suna a harkokin yawon shakatawa a lokacin zafi. Yanayi mai dan sanyi na wajen a duk tsawon shekara ya fi faranta rayukan mutane.
Kasar Sin ta shirya tsarin kimanta biranen yawon shakatawa ta fuskar gudun zafi ne bisa ma'aunin Guiyang. Hakan ya nuna fifikon da halin musamman na wannan birni a fannin yanayi. Ge Yujing, mataimakin shugaban hukumar yawon shakatawa ta birnin Guiyang ya bayyana cewa,"A shekarar 2009, birninmu na Guiyang ya zama daya kacal a nan kasar Sin da ke shiga jerin birane 10 ta fuskar rashin zafi a duk duniya. Ban da wannan kuma, a nan kasar Sin, birninmu ya yi shekaru 5 a jere yana kan gaba a tsakanin biranen da suka fi rashin zafi. Ta haka in an nemi bambanci birninmu da wasu biranen yawon shakatawa, to, yanayin Guiyang shi ne alamarsa."
Haka kuma, yanayin kasa mai sigar musamman ya bambanta Guiyang da sauran sassan kasar Sin. Ana iya samun tsarin yanayin kasa na Karst mai ban sha'awa a wurin shakatawa na Tianhetan da ke da nisan kilomita 22 daga birnin Guiyang a kudu maso yammaci. Ni'imtattun wurare masu ban mamaki sun sanya mazauna wurin su fito da labaru masu ban sha'awa da yawa. Sun tsara mabambantan labaru bisa kogunan dutse da duwatsun stalactites masu siffofi daban daban, sun siffanta wa maziyarta wata duniya mai ban mamaki.
A birnin Guiyang, akwai wuraren shakatawa da yawa, kamar rafin Huaxi da tabkin Baihuahu da wurin nishadi na Xiuwen Yangming.
Bayan haka kuma, maziyarta kan kai ziyara ga wuraren tarihi a birnin Guiyang. Gidan ibada na Hongfusi da aka gina a shekarar 1672 yana daya daga cikin irin wadannan wuraren tarihi, inda akwai sufaye da yawa da suke gudanar da harkokin addini a can.
Yau shekaru 340 ko fiye da suka wuce wato a zamanin da sarki Kangxi na daular Qing yake mulkin kasa, wani mai bin addinin Buddha dattijo mai suna Chisong ya je Guiyang, ya gano cewa, akwai kungurmin daji na gorori a babban tsaunin Qianlingshan a kuryar arewa maso yammacin birnin Guiyang, ya dace da nazari da yada addinin Buddha matuka. Ta haka ya yi kokarin tara kudi, ya gina wani gidan ibada mai suna Hongfusi a babban tsaunin. Ba da jimawa ba gidan ibada na Hongfusi ya fara shahara, ya zama shahararren gidan ibada a lardin Guizhou, har ma a duk kasar Sin. Shi Tongdi, mai bin Buddha da ke kula da karbar baki a wannan gidan ibada ya gaya mana cewa, kawo yanzu mabiya addinin Buddha na gidan ibada na Hongfusi suna gudanar da harkokin yau da kullum ta hanyar da suka saba bi a tsanake. Inda ya ce,"A ko wace rana, mu kan fara ne ta hanyar da muka saba ta fannin addinin Buddha. Mu kan buga kararrawa a ko wace rana da safiya misalin da karfe 4 da rabi, bayan mintoci 30, mu kan buga ganga har na tsawon mintoci 10, a daidai wannan lokaci, manbiya addinin Buddha kan taru a babban zaure, inda suke fara karanta da nazari kan littattafan addinin Buddha. Haka kuma mu kan fara buga ganga da misalin karfe 8 na dare a ko wace rana, daga baya, mu buga kararrawa, sa'an nan mu buga katako. Bayan hakan, mu kan fara darasinmu na dare."
Ana iya sauraran amon ganga da kararrawa a duk babban tsaunin Qianlingshan, amon kan sanya wurin nishadi na babban tsaunin Qianlingshan ya kara nuna sha'awa. Wurin nishadi na babban tsaunin Qianlingshan ya yi suna ne a sakamakon kyakkyawan babban tsauni da ruwa da kungurmin daji maras hayaniya da gidan ibada mai dogon tarihi da idon ruwa mai tsarki da birai masu hikima. Wannan wurin nishadi na arewa maso yammacin yankin tsakiyar birnin Guiyang, ba tsananin sanyi da tsananin zafi a wajen, ta haka ya zama wuri mafi dacewa da mazauna wurin ta fuskar yin yawo da motsa jiki. Xu Yongmei, mai yi wa maziyarta bayani a wurin nishadi na babban tsaunin Qianlingshan ta bayyana cewa, a ganinta, ta taki sa'a da samun aikin yi a wurin nishadin. Inda ta ce,"Ma iya cewa, na taki sa'a. In mun dade mun aiki a nan, za mu samu tsawon rai. Wani abokin aikina yana zaune a unguwar gidajen ma'aikatanmu a kasan babban tsaunin Qianlingshan, shekarunsa sun wuce dari a duniya, ya zuwa yanzu yana cikin koshin lafiya. Yanayi a wurin yana amfanawa wajen kiwon lafiya."
Birnin Guiyang birni ne da kabilu da dama suke zaune tare, kuma 'yan kabilar Han sun fi rinjaye. Ta haka, ana iya kara fahimtar ire-iren bukukuwan gargajiya da 'yan kabilu daban daban suka saba shiryawa.
A cikin al'adun gargajiya da lardin Guizhou ke da su, akwai wani irin wasan kwaikwayo mai suna Dixi ko kuma Tanxi, wanda aka mayar da shi a matsayin asalin wasan kwaikwayon kasar Sin. Mazauna wurin sun gaya mana cewa, yau shekaru dari 6 ko fiye da suka wuce, bisa umurnin sarki Zhu Yuanzhang da ke mulkin kasar Sin a zamanin daular Ming, kakanin-kakaninsu sun je yankin kudu maso yammacin kasar domin yaki da sojojin zamanin daular Yuan. Bayan da suka yi nasara, suka fara zama a wurin, inda suke gudanar da ayyukan noma, kuma sun kira wannan wurin da suke rayuwa da sunan Tunbao. Har zuwa yanzu ana ci gaba da bin al'adun gargajiya daban daban da kakanin-kakaninsu 'yan kabilar Han suka taba bi tun zamanin daular Ming.
Yanzu haka dai, matasan da ke zaune a Tunbao suna son karbar baki da hannu bibbiyu. In sun yi baki, su kan samar musu shayi da giya masu dadi. Haka kuma, su kan rera wakoki masu dadin ji domin maraba da wadanda suka zo daga wurare masu nisa.
A hakika a kewayen birnin Guiyang, da akwai wuraren shakatawa fiye da 30 da wuraren tarihi 8 da shiyyoyin kiyaye halittu 4 da kuma shahararrun birane 2 masu dogon tarihi da suka yi suna ta fuskaar al'adu. Sinawa kan ce, kyawawan biranen Suzhou da Hangzhou sun yi kama da Aljanna, kuma birnin Guiyang ya yi fice domin yanayi mai kyau. (Tasallah)