in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dandana tsantsar abinci irin na Sichuan a birnin Chengdu da ya shahara ta fannin abinci mai dadi
2010-06-20 18:39:02 cri
Masu karatu, barka da war haka! Tasallah ce ke yi muku marhabin cikin shirinmu na "Ina so in je lardin Sichuan". A kwanan baya, a hukumance birnin Chengdu, babban birnin lardin Sichuan ya sami iznin shiga tsarin birane da suka yi fice ta fannin kirkire-kirkire da hukumar kula da ilmi da kimiyya da al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNESCO ta kafa, inda aka mayar da shi a matsayin birnin abinci mai dadi, wato birnin da ya shahara ta fuskar abinci mai dandano. Ta haka birnin Chengdu ya zama na farko a nahiyar Asiya da ya kasance birnin abinci na duniya. Wasu kan ce, in ana son cin abinci, to, ya fi kyau a je kasar Sin, inda kuma ake samun abinci mafi dandano a lardin Sichuan. Abinci irin na Sichuan na da dogon tarihi, haka kuma, abincin da ake samarwa a Chengdu ya yi suna matuka a gida da wajen kasar Sin. Yau za mu je birnin Chengdu da ke lardin Sichuan, inda ake samun asalin abinci irin na Sichuan a wajen, kuma yana matsayin wata cibiya ce ta fannin raya abinci. Kafin mun more baki da abinci mai dadi, za mu gabatar muku da wata tambaya, don Allah kun gaya mana sunan wani nau'in abinci irin na Sichuan.

Lardin Sichuan aljanna ce ta bangaren abinci mai dadi a wajen Sinawa. A matsayinsa na daya daga cikin manyan hanyoyin dafa abinci guda 4 a nan kasar Sin, abinci irin na Sichuan ya shahara a gida da kuma waje bisa hanyar dafa abinci da ta sha bamban da saura da kuma dandano na musamman na abincin. Kuku-kuku su kan yi amfani da abubuwa iri daban daban wajen dafa abinci irin na Sichuan, kuma akwai mabambantan dandano ta fuskar abinci irin na Sichuan, amma mazauna Sichuan sun fi son kayan abinci mai yaji. Har ma in an ambaci abinci iri na Sichuan, to, nan da nan sai a tuna da kayan abinci mai yaji da kamshi. Amma donme mazauna Sichuan suke son kayan abinci mai yaji? Dalilin kuwa shi ne Sichuan ya kasance cikin wani kwari, kuma akwai danshi sosai a wurin, masoro da barkono suna taimakawa wajen kiyaye mutane daga danshi da kamuwa da ciwon amosanin kashi da sauran munanan cututtuka, ta haka ake gadon abinci irin na Sichuan mai yaji daga zuriya zuwa zuriya a wurin.

Bisa kwarya-kwaryar kididdigar da aka samu, an ce, akwai nau'o'i fiye da dubu 4 na abinci irin na Sichuan. Wadanda ke iya wakiltar abinci irinsu Gong Bao Ji Ding da aka dafa da naman kaji da Zhang Cha Ya da aka dafa da naman agwagwa da Hui Guo Rou da Yu Xiang Rou Si da aka dafa su da naman alade da dai makamantansu. An sa muhimmanci kan wadannan kayayyakin abinci ta fannonin launi da kamshi da kuma dandano. Li Wei, mai dakin cin abinci mai suna Hong Xing da ya fi shahara a Chengdu ta fannin dafa abinci irin na Sichuan ya gaya mana cewa,"Hui Guo Rou da aka dafa da naman alade, da Mapo Tofu da aka dafa da wani irin nau'in abincin da aka samu daga wake, da Gong Bao Ji Ding da aka dafa da naman kaji su ne wadanda suka fi nuna siga ta musamman ta lardin Sichuan, kuma sun shahara kwarai da gaske. Dimbin abokaina da suka fito daga sauran sassan kasar Sin suna son wadannan kayayyakin abinci a lokacin da suke yin ziyara a Chengdu. Zabar danyun abubuwan da ake amfani da su wajen dafa Gong Bao Ji Ding na da matukar muhimmanci. Tilas ne a yi amfani da kajin da ake kiwonsu ba tare da abincin dabbobi ba. Kuma kayan abincin ya zama na da yaji kadan da zaki da kuma dan tsami."

Kamar yadda kayan abinci na Gong Bao Ji Ding yake, dafa yankakken nama da ganyaye a tukunya wato Huoguo shi ma ya yi suna sosai. Wasu kan ce, in ba ka ci Huoguo ba, to, ma iya cewa, ziyararku a Sichuan ta zama banza. Mazauna Sichuan na sha'awar Huoguo ainun. Suna son zama a kewaye wata tukunya a kan tebur, inda suke dafa miya mai cike da kayayyakin kamshi masu nau'o'i daban daban, daga baya su kan saka danyun abubuwan abinci cikin ruwan, har sai sun dafu, sa'an nan su kan tsoma su cikin miya mai cike da yaji da barkono da gishiri da man girke mai kamshi da aka samu daga ridi. Huoguo kan faranta rayukan mutane kwarai, kuma mutane kan kece raini wajen cin Huoguo tare. Wang Lilin, wata sabis ce da ke aiki a shahararren dakin cin Huoguo a Chengdu, wato Xiao Tian E ta yi karin bayani da cewa,"Huoguo kan jawo hankalin mutane sosai, kuma ya kan karfafa gwiwar masu cin abinci. Ana iya dafa danyun yankakken nama da ganyaye mabambanta a cikin tukunya. Haka kuma, miyar da ake amfani da ita domin dafa abincin ta kan hada da danyun laimar kwadi da wasu halittun kungurmin daji masu wuyar samuwa, wadanda ke taimakawa wajen kishin lafiyar mutane. Haka zalika, a kan dafa kashi da magunguna sosai da sosai cikin ruwa a yayin da aka shirya cin Huoguo, saboda su ma suna taimakawa wajen kishin lafiyar mutane. Ban da wannan kuma, a kan dafa yankakken naman sa da tunkiya da kifi da kayan cikin sa cikin tukunya. Bayan haka, a kan dafa danyun kifaye cikin ruwa domin shirya dafa Huoguo, da samun miyar mai kamshi."

Madam Wang ta kara da cewa, hanyar da aka saba wajen cin Huoguo ita ce kewaye wata babbar tukunya tare da dafa yankakken nama da ganyaye tare. Hakan kan sa a cika da murna matuka. Duk da haka, yanzu ko wane mutum kan dafa yankakken nama da ganyaye cikin wata karamar tukunya, ba su ci cikin tunkuya daya tare. Wannan yana da tsabta, kuma kowa na iya cin duk abin da yake so cikin tukunyar, ta haka wannan salo ya samu karbuwa ainun a tsakanin matasa.

A hakika, cincin da sauran kayan ciye-ciye danginsa irin na Chengdu su ma suna matsayin daya daga cikin nau'o'in abinci irin na Sichuan. Dimbin nau'o'in cincin irin na Chengdu kan shiga zukatan masu sha'awar cin abinci da yawa.

Masu karatu, in kun duba bayanan da suka shafi abinci irin na Sichuan a shafin Internet, ba tare da wata matsala ba kuna iya gano wani shafin Internet mai suna Chuan Wei Fang. Wasu matasa masu sha'awar abinci irin na Sichuan su ne suka bude shafin, da nufin kara yayata dandanon abinci irin na Sichuan bisa sha'awar da suke nunawa kan abincin garinsu. Hu Bin, mai kula da shafin ya yi bayani da cewa, "Muna gai da dimbin masu sha'awar abinci da kuma wadanda suka yi fice wajen dafa abinci bisa sirrinsu. Ba kayan abinci ko kuma Huoguo da ke iya wakiltar dandanon abinci irin na Sichuan kawai ba, har ma dukkan abubuwan da suka shafi abincin, kamar asalin abinci da zabar danyun abubuwa da dai sauransu suna nuna siga ta musamman. Muna sha'awarsu kwarai da gaske. Mu matasa ya kamata mu sami imanin yayata karin fitattun abubuwan da garinmu ke samarwa. Haka kuma, muna sha'awar cin abinci, wannan ya sa muka bude shafin"

A shafin Chuan Wei Fang, kuna iya kara fahimtar kayayyakin abinci irin na Sichuan da suka fi shahara da labarun tarihi da samun dakunan cin abinci da suka fi shahara ta fannin abinci irin na Sichuan ko kuma kananan shagunan da suke samar da tsantsar abinci, haka kuma, kuna iya fahimtar fitattun abubuwan al'adu da suka shafi abinci mai dadi. Hu Bin ya ce,"Mutane suna sha'awar nazarin abinci a lokacin hutu, musamman ma tsoffafi. Matan aure da yawa da ke zaune a yankunan karkara kan yi nazarin abinci a lokacin hutu. Bayan da suka fito da sabbin kayayyakin abinci, su kan yayata su a tsakanin abokansu, in sun samu karbuwa, to, sai su kara yayata su."

An samu asalin abinci irin na Sichuan ne daga dakunan dafa abinci na fararen hula. In kun sami damar ziyartar Chengdu, tabbas ne za ku samu dandanon da ya fi burge ku a titunan birnin Chengdu.

To, masu karatu, kafin mu sa aya ga shirinmu na yau, bari in maimaita tambayarmu, don Allah ku gaya mana sunan wani kayan abinci irin na Sichuan. Madalla, karshen ziyararmu a Sichuan a yau ke nan. Tasallah da na gabatar muku da shirin, nake cewa, ku huta lafiya.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China