Babban tsaunin Meihuashan da ke birnin Nanjing na lardin Jiangsu yana daya daga cikin shahararrun wuraren da suka fi dacewa da kallon furannin Meihua a nan kasar Sin. A duk farkon lokacin bazara, dubban itatuwan Meihua na layi layi suna fid da furanni, sai ka ce gajimaren furannin Meihua. Dimbin maziyartan da suka fito da gida da wajen kasar Sin sun ji dadin kyan muhallin da suke kasancewa, har ma ba su so komawa gida.
A karshen watan Febrairu zuwa farkon watan Maris na ko wace shekara, wato a daidai lokacin da aka fid da furannin Meihua, a kan shirya shagalin kallon furannin Meihua a birnin Nanjing. Yau bari mu yi yawo a babban tsaunin Meihuashan tare.
A gabas da dakin kallon furannin Meihua, wato Guanmeixuan da aka gina a babban tsaunin Meihuashan, akwai itatuwan Meihua 2 masu tsawon shekaru dari daya, ana kiransu da sunan "Qingrenmei", wato itatuwan Meihua da suka yi kaman masoya wato Qingren a Sinance. Wadannan itatuwa 2 da suka fid da furanni masu tarin yawa kan jawo hankalin maziyarta da yawa. Gong Qinghua, babbar mai yin hasashen yanayin furannin Meihua a babban tsaunin Meihuashan ta yi mana bayani kan asalin wadannan itatuwan Qingrenmei."Donme ake kiran wadannan itatuwan Meihua da sunan 'Qingrenmei'? Dalilin shi ne kowa na iya gano cewa, su itatuwa 2 ne, babbar da karamar sun dogara da juna, kuma sun rungumi juna, sai ka ce masoya suna rungumi juna. Sa'an nan su kan fid da furanni a ko wane watan Febrairu, wato a daidai ranar masoya ta ko wace shekara, sun kasance cikin hali mafi kyau wajen fid da furanni. Tun zamanin da, Sinawa suka yayata labarin tarihi na cewa, matasa maza da 'yan mata su kan tabbatar da soyayya a tsakaninsu bisa alamar furannin Meihua. Wannan shi ne dalilin da ya sa a ko wace ranar Masoya, masoya da yawa kan dauki hotuna a dab da wadannan itatuwa 2."
Yanzu an shiga lokaci mafi dacewa da kallon furannin Meihua a babban tsaunin Meihuashan. Gong Qinghua mai kirki ta gabatar wa maziyarta hanyar da ta fi dacewa wajen more ido da furannin Meihua. Tana mai cewa,"In maziyarta suna son kallon furannin Meihua a farkon watan Maris, to, na shawarce su da bi hanyar da aka saba bi wajen kallon furannin, wato za ku yi yawo daga mutum-mutumin dutse da ke titin Shixianglu zuwa dakin Boaige. Saboda wannan wuri na kasancewa a jikin tsaunin, itatuwan Meihua da aka shuka a wajen na iya fuskantar rana, ta haka su kan dauki jagoranci wajen fid da furanni. Babu tantama in kun yi yawo daga dakin Boaige zuwa fadar Shouxinggong, za ku iya ganin itatuwan Meihua da su kan dauki jagoranci wajen fid da furanni. A kwanaki 10 na farkon watan Maris a bana, more ido da wadannan kyawawan furanni zai iya faranta rayukanku sosai."
A shekarar da muke ciki, a gabannin bikin Bazara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, an yi dusar kankara da bala'in daskarewa a kudancin kasar Sin. Bala'un sun lalata furannin Meihua da ke lambunan renon itatuwan Meihua da yawa, amma a babban tsaunin Meihuashan da ke birnin Nanjing, itatuwan Meihua sun tsira daga munanan bala'un, sun yi toho, kuma bayan da kankara da dusar kankara suka narke, dukkan halittu sun farka domin zuwan lokacin bazara, itatuwan Meihua sun fara fid da furanni. Zhu Jun, mai yin hasashen halin da furannin Meihua ke ciki a babban tsaunin Meihuashan, kuma wani abokin aikin madam Gong ya yi bayani da cewa,"Ma iya cewa, itatuwan Meihua da aka samu a babban tsauninmu na Meihuashan sun tsira daga bala'in dusar kankara a wannan shekara. Furannin Meihua sun tsira daga iska mai tsananin sanyi, yanzu yanayi na kara samun dumi, furannin Meihua sun kiyaye kyan surarsu. A shekarar da muke ciki, itatuwan Meihua da aka samu a babban tsauninmu sun fid da furanni a daidai lokaci. An kiyasta cewa, a karshen watan Maris, yawancin itatuwan Meihua za su fid da furanni."
Baya ga furannin Meihua da ake samu a duk babban tsaunin Meihuashan, an nuna harkokin wasanni da al'adu daban daban daya bayan daya a wannan babban tsauni. Tun daga karshen watan Febrairu zuwa kwanaki 10 na tsakiyar watan Maris na ko wace shekara, a kan nuna wasannin raye-raye da wake-wake na 'yan kananan kabilu har sau 12 a babban tsaunin Meihuashan a birnin Nanjing. Wang Pengshan, shugaban hukumar kula da harkokin makabartar da aka binne Sun Zhongshan, wani shahararren dan siyasa na kasar Sin ya yi karin bayani da cewa,"Shagalin kallon furannin Meihua na kasa da kasa da muke shiryawa a bana shagali ne a karo na 15 da a kan yi a birninmu na Nanjing. Mun shirya kasaitattun bukukuwan al'adu, kaman manyan tarurruka 5 na nune-nunen zane-zane da rubuce-rubuce, wadanda aka yi da fatan yayata kyan surar furannin Meihua. Ta haka mu mazauna birnin Nanjing gami da maziyatan da suka fito daga gida da wajen kasar Sin dukkansu suna iya jin dadin wadannan bukukuwan al'adu."
Itatuwan Meihua da suka fid da furanni sosai da sosai da wasannin raye-raye da wake-wake masu kayatarwa da 'yan kananan kabilu suka nuna da kuma kyan yanayi sun karfafa gwiwar maziyarta da mazauna wurin su yi yawo. Ga shi wani mai yawon shakatawa ya yi mana bayani da cewa,"Yau ana rana sosai. Na yi yawo a babban tsaunin Meihuashan tare da iyalina. Wasannin al'adu da ake nuna suna da ban sha'awa matuka. Ina farin ciki sosai. Ina fatan a wannan shekara, aiki zai yi kyau a gare ni, kuma duk iyalina za su kasance cikin koshin lafiya."
Birnin Nanjing birni ne mai cike da so. Shagalin kallon furannin Meihua da a kan yi a ko wace shekara ya yi kama da manzon sanar da zuwan lokacin bazara, wanda ya kan kirawo abokai. Maziyartan da suka zo daga gida da wajen kasar Sin sun je birnin Nanjing mai dogon tarihi da zummar jin dadin kyan surar lokacin bazara. Ji Jianye, magajin birnin Nanjing ya ce,"Muna more ido da wadannan itatuwan Meihua da suka fid da furanni duk da tsananin sanyi. Su ne manzon sanar da zuwan lokacin bazara. Yanzu lokacin bazara ya yi. Bari mu shaki kamshin furannin Meihua masu tarin yawa, tare da fahimtar sigar musamman da birninmu na Nanjing take da ita."(Tasallah)