in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yin yawo a babban tsaunin Qixiashan a lokacin bazara
2010-06-20 18:39:02 cri
A birnin Nanjing na kasar Sin, akwai wani zance na cewa, babban tsaunin Niushoushan ya dace a kai masa ziyara a lokacin bazara, da ma na kaka, babban tsaunin Qixiashan ya kan kasance abun sha'awa wajen kallo, saboda jajayen ganyayen itatuwan Maple. A karshen lokacin kaka, jajayen ganyayen itatuwan Maple su kan yi kama da hasken wuta, kuma suna rufe duk wannan babban tsauni wajen, suka kasance tamkar lokacin faduwar rana da ya haska kan babban tsaunin Qixiashan. Wannan shi ne dalilin da ya sa wannan babban tsauni ya samu sunansa na "Qixia", wato hasken rana kan babban tsauni a lokacin faduwar rana. Babban tsaunin Qixiashan ya yi suna ne saboda jajayen ganyayen itatuwan Maple masu abin sha'awa, kamar na babban tsaunin Xiangshan da ke birnin Beijing, ko na Yuelushan da ke lardin Hunan, da na Tianpingshan da ke birnin Suzhou.

Amma babban tsaunin Qixiashan kan fitar da kyan surarsa ta musamman ne a lokacin bazara. Idan an je babban tsaunin Qixiashan ziyara a lokacin kaka, ana iya ganin jajayen ganyayen itatuwan Maple da suka yi kama da hasken wuta sun rufe duk wannan babban tsaunin. Amma a lokacin bazara kuma, ana iya ganin irin wadannan kyawawan jajayen ganyayen ba tare da zato ba. Da zarar an shiga farfajiyar wurin shan iska na babban tsaunin Qixiashan, to, ana iya ganin wasu itatuwan Maple da ke da jajayen ganyaye. Amma in an ci gaba da tafiya, ana iya cin karo da dimbin korran itatuwa masu yawa. Wannan ba wani sauyi ba ne. Bayan an ci gaba da 'yan tafiyar mita dari daya ko biyu, a kwana ta hanyar, ana iya ganin jajayen ganyayen itatuwan Maple da yawa. Ana kiran wannan wuri da sunan "Shuang Hong Yuan". An samu wannan suna ne daga wata rubutacciyar wakar da aka rubuta yau shekaru fiye da 1400 da suka wuce, wato a zamanin daular Tang ta kasar Sin. Maziyartan da kan zazzagaya a babban tsaunin kan ji mamaki sosai da ganin jajayen ganyayen itatuwan Maple. Wani da ya ziyarci wajen ya bayyana cewa,"A daidai wannan lokaci, kyan surar babban tsaunin Qixiashan ta kan sha bamban da yadda take a lokacin kaka, a wancan lokaci, jajayen ganyayen itatuwan Maple su kan rufe dukkan tsaunin. A ganina, tattaki kan samar mana sakin jiki, kuma muna jin dadi sosai. A lokacin bazara, muna iya ganin jajayen ganyaye itatuwan Red Maple, kamar yadda mu kan gani a lokacin kaka."

Launin ganyayen irin wadannan itatuwan Red Maple kan yi ja tun bayan da suka toho, har zuwa lokacin faduwarsu. Tun da can, ana iya samun wasu itatuwan Red Maple a babban tsaunin Qixiashan. Yau shekaru fiye da 10 da suka wuce, masu kula da wurin shan iska na babban tsaunin Qixiashan sun fara sa muhimmanci kan dasa karin itatuwan Red Maple. Amma ba a samu irin wadannan itatuwa da yawa ba a wajen, haka kuma, su kan dauki dogon lokaci wajen girma, wannan ya sa itatuwan Red Maple sun kara daraja, in an kwatanta su da sauran nau'o'in itatuwan Maple. Na san wani bayanin da ke cewa, sauyin launin ganyayen itatuwan Maple alama ce ta nuna tsawon ran ganyayen, dan haka a lokacin kaka, ganyayen itatuwan Maple kan zama ja ne daidai lokacin da suke dab da mutuwa. Sa'an nan a lokacin bazara, ganyayen itatuwan Red Maple su kan yi toho, launinsu ya zama ja mai haske. A game da wannan, Li Hong, darektan ofishin kula da harkokin wurin shan iska na babban tsaunin Qixiashan ya shedar da cewa,"In an kwatanta jajayen ganyayen itatuwan Maple wadanda mu kan gani a lokacin kaka da wadanda mu kan gani a lokacin bazara sun fi kyan gani. Saboda a lokacin bazara ba su dade da tohowa ba, launinsu kan zama ja mai haske, kuma ba a yi musu barna ba. Bayan lokacin zafi, watakila an barnata ganyayen, ko kuma wasu kwari sun yi musu lahani, ko kuma cututtuka sun kama ganyayen. Amma a halin yanzu, ganyayen na da cika."

Masu karatu, in kuna da sha'awa, ya dace ku ziyarci babban tsaunin Qixiashan domin kara fahimtar irin kyan surar wadannan jajayen ganyayen itatuwan Maple a lokacin bazara. Kai! Na kusa mantawa da wani sirri. Masu sauraro, a lokacin da kuke more kallon jajayen ganyayen, ya fi kyau ku fuskanci hasken rana, ta haka launin ganyayen kan zama ja mai haske.

A hakika, akwai wani wurin da ya fi kyau a kai masa ziyara a babban tsaunin Qixiashan, wato gidan ibada na Qixiasi mai tsawon shekaru 1600 ko fiye. An fara gina shi a shekarar 483 bayan haihuwar Annabi Isa A.S.. A zamanin daular Tang, wato daga shekara ta 618 zuwa ta 907, an bunkasa da kuma fadada shi. Tun can da har zuwa yanzu, a ko wace ranar jajibirin sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, mazauna birnin Nanjing kan taru a gidan ibada na Qixiasi, inda su kan buga kararrawa da zummar samun alheri, sa'a da kwanciyar hankali a sabuwar shekara.

Haka zalika, akwai dukiyoyi 3 a cikin wannan gidan ibada na Qixiasi, wato hasumiyar ajiye kashin tsoffin mabiya addinin buddha, da kogunan dutsen da aka sassaka mutum mutumin Buddha da yawa a ciki, da kuma wani dutsen da aka sassaka bakaken Sinanci a kansa. Ko wannensu na da nasa dogon tarihin. A cikinsu kuma, dutsen da aka sassaka bakake a kansa ya fi yin suna. An samar da wannan dutse a shekara ta 676, wato yau shekaru 1300 ko fiye da suka wuce. An ce, sarakunan zamanin daular Tang na kasar Sin sun kafa wannan dutse ne domin yi wa wani mabiyin addinin buddhan da ke cikin gidan ibada na Qixiasi godiya. Zhao Jun, kwararre ne mai nazarin tarihin gidan ibadan na Qixiasi ya bayyana cewa,"Wannan dutsen da aka sassaka bakake a kansa a zamanin daular Tang ya zama wanda aka fi adana shi cikin yanayi mai kyau a birnin Nanjing. An sassaka bakake guda 2376 a kansa. Sakamakon adana shi da muke yi ta hanyar da ta dace, ya sa duk tsawon lokacin, nan wasu bakake 13 ne kawai daga cikin wadanda aka rubuta suka bace. Baya ga hakan, akwai dimbin fararen zane-zanen furannin Plum Blossom wato Meihua a Sinance a kan dutsen, dan haka masu bautawa addinin buddhan gidan ibadan kan kira dutsen da sunan 'Meihuashi', wato dutsen da aka samu zane-zanen Meihua a kansa. Dutsen Meihuashi na daya daga cikin duwatsu guda 10 masu ban mamaki a birnin Nanjing. Kwararru masu nazarin kayayyakin tarihi sun tabbatar da cewa, fararen zane-zanen da ke kan dutsen Meihuashi gawawaki ne na wani nau'in tsiron da ke a cikin teku yau shekaru miliyan 280 da suka wuce. Yawan gawawakin ya wuce dubu 20. Wannan ya sa irin wannan dutse na da wuyar samuwa matuka. Ban da wannan kuma, a bayan dutsen, wani sarki a zamanin daular Tang na kasar Sin ya rubuta bakaken 'Qixia', dan haka a kan kira dakin da ake ajiye wannan dutse da sunan 'Yubeiting'."

Dutsen Meihuabei yana daidai gaban babbar kofar gidan ibada na Qixiasi. Masu bautawa addinin buddha suna kyautata kula da shi.

An ce, akwai wuraren yawon shakatawa fiye da 30 da aka rubuta tatsuniyoyi masu ban sha'awa a game da su a wannan babban tsaunin. Kamar yadda Sinawa kan ce, gani ya kori ji, ya fi kyau a kai masa ziyara, a ziyarci wannan kyawawan wurare tare da jin tatsuniyoyin. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China