in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kara fahimtar kyan surar wuraren da ke kudu da kogin Yangtse a lardin Jiangsu
2010-06-20 18:39:02 cri
Za a yi bikin baje koli na kasa da kasa a birnin Shanghai na kasar Sin a wata mai kamawa. A wancan lokaci, tabbas ne miliyoyin maziyarta daga sassa daban daban na duniya za su hallara a farfajiyar bikin. Amma birnin Shanghai ba zai gamshe su ba, watakila su so ziyartar wasu kyawawan wurare a Sin.

Ba damuwa! Hukumomin kula da harkokin yawon shakatawa na kasar Sin sun gabatar da shirye-shiryen suka shafi yawon shakatawa. Yau za mu yi kokarin kara ilmi kan lardin Jiangsu da ke dab da Shanghai ta arewa. In an sami damar kai ziyara lardin, ya fi kyau da farko a ziyarci birnin Nanjing, wanda shi ne babban birnin lardin. A ganin Sinawa, birnin Nanjing, birni ne da ake iya fahimtar yanayi mai kyau ta fuskar al'adun gargajiya na kasar Sin.

Birnin Nanjing na daya daga cikin manyan birane 4 masu dogon tarihi na kasar, kana kuma daya ne daga cikin shahararrun birane a harkokin al'adu da tarihi a kasar. Tsawon shekarunsa ya wuce dubu daya. Kafin an shiga birnin na Nanjing, ya fi dacewa a zaga ganuwar da ke kewayen Nanjing, wadda aka gina yau shekaru dari 6 ko fiye da suka wuce, wato a zamanin daular Ming ta kasar Sin. Tsawon ganuwar da aka tattala ta har zuwa yanzu ya kai misalin kilomita 23. Ita ce ganuwa mai dogon tarihi kuma mafi tsawo da ake kula da ita cikin yanayi mai kyau a duk duniya. Kara fahimtar wannan ganuwa yana iya taimakawa wajen kara fahimtar al'adun kasar Sin masu dogon tarihi, wadanda ke da tsawon zamani.

In an kai ziyara a birnin na Nanjing, gidan ibada na Fuzimiao da kuma kogin Qinhuaihe su ne ni'imtattun wuraren da ya kamata ka je don ziyartarsu.

Gidan ibada na Fuzimiao gidan ibada ne da aka gina yau shekaru kusan dubu daya da suka wuce, domin girmama Confucius, wato Kongzi ta bakin Sinawa, wanda dattijo ne ta fannin tunani da tarbiya a zamanin da a kasar Sin. Gidan ibadan Fuzimiao da gine-gine da ke cikinsa masu fadi sun dade a tarihin birnin Nanjing. Kwaskwarimar da aka yi musu a tsanake ta sanya surorinsu sun kara kyautata.

Mutanen Sin kan siffanta kogi a matsayi mahaifa. A birnin Nanjing, a kan mayar da kogin Qinhuaihe tamkar mahaifar Nanjing. A gefuna 2 na wannan kogi na Qinhuaihe, akwai ni'imtattun wurare da wuraren yawon shakatawa da ba za a iya kidaya yawansu ba. Ana iya kara fahimta kan al'adun birnin Nanjing masu tsawon tarihin shekaru dubu 2 ko fiye a lokacin da ake yin ziyara a kogin. Kana kuma, shi ne alamar Nanjing ta nuna wadata. Ga wata kyakkyawar budurwa da ke jagorantar maziyarta tana karin bayani kan sigar musamman da gine-ginen da ke gefuna 2 na kogin Qinghuaihe suke da ita, inda ta ce,"In kun kalli gine-ginen da ke gefuna 2 na kogin, za ku iya gano cewa, gine-ginen sun sha bamban da wasu. An gina su ne ta la'akari da salon gine-gine na lardin Anhui. Bangwaye da kwanukan rufi na gine-ginen ba kawai suna da kyan gani ba, har ma suna ba da taimako wajen kare gine-ginen daga gobara da tsananin sanyi da na zafi."

Sinawa kan ce, yin tafiya a kan kogin Qinhuaihe cikin kwale-kwale da dare ya zama tamkar tambarin Nanjing ta fannin yawon shakatawa. A gefuna 2 na kogin, akwai wasu shahararrun wuraren shan iska, da filin jarrabawa mafi girma da aka gina a zamanin da na kasar Sin. Haka zalika, ana iya ziyartar gidajen da shahararrun marubuta na zamanin da na kasar Sin suka taba zama a ciki.

Baya ga birnin Nanjing, ya fi kyau a kai wa karamin birnin Yixing ziyara. Kuma in an je Yixing, ya dace ka kewaya yankunan karkara. Wannan karamin birni ya yi kama da zane-zanen gargajiya irin na kasar Sin. Akwai gonakin shuka itatuwan ganyen shayi masu fadi da gine-gine sirara da kuma dimbin gorori. Malama Huang, wadda ke jagorantar maziyarta ta yi bayani da cewa,"Birnin Yixing yana kuryar kudu ta lardin Jiangsu, inda ake samun filin gorori masu fadin murabba'in kadada dubu 15. An dasa a kan gangarar manyan tsaunuka, ba a iya ganin iyakar filin gorori a takaice, sai ka ce tekun gorori. Birninmu na dab da manyan tsaunuka da koguna, ta haka a ko ina ana iya ganin kyawawan wurare. Sa'an nan a wani lambun renon gorori mai suna 'Baizhuyuan', ana iya samun gorori masu nau'o'i fiye da 150. A daidai wannan lokaci, ana iya hakar kananan kananan tsirran gorori a wajen."

Masu karatu kada ku tsaya a Yixiang kawai, ya fi kyau ku ci gaba da tafiya. Birnin Suzhou da ake iya zuwa daga Shanghai cikin awa guda kawai yana daya daga cikin wuraren da ke jawo hankalin wadanda suke da nufin halartar bikin baje koli na duniya da za a yi a Shanghai. A cikin rubutaccen tarihi, tsawon tarihin Suzhou ya wuce shekaru dubu 4. Ya dade yana shahara saboda kyawawan manyan tsaunuka da koguna da kuma lambunan shan iska. An saka lambunan shan iska guda 9 da ke birnin cikin jerin sunayen wuraren tarihi na al'adu na duniya. Deng Jiachen, wanda ke aiki a lambun shan iska na Shizilin a Suzhou ya yi alhafari da lambunsa, inda ya ce,"Galibin lambunan shan iskar da ke birnin Suzhou sun kasance masu zaman kansu, inda ake iya ganin kananan gadoji, rafuka, manyan duwatsun da aka jera, dakuna, da kuma hasumiyoyi a lokaci guda. Alal misali, a lambunmu na Shizilin, jerin manyan duwatsun da aka jera su kan jawo dimbin maziyarta daga gida da wajen kasar Sin. Shahararren sarki Qianlong na zamanin daular Qing ya yi rangadin aiki sau 6 a yankunan da ke kudu da kogin Yangtse. A ko wane karo, ya kan je lambun shan iska na Shizilin, har ma ya taba rubuta wakoki a game da shi."

Galibi dai a cikin shirye-shiryen yawon shakatawa da aka gabatar a game da bikin baje koli na duniya da za a yi a Shanghai, akwai wurare masu kyan gani da yawa da ke birnin Suzhou. Maziyarta na gida da wajen kasar Sin za su samu damar tsokale kwarakwatan idanunsu da wuraren shakatawa masu sigar musamman ta kasar Sin, baya ga ziyartar kasaitaccen bikin da za a yi a Shanghai.

Kasar Sin na maraba da baki da hannu bibbiyu, musamman ma wuraren da ke makwabtaka da birnin Shanghai. Yuan Ding, mataimakin shugaban hukumar kula da harkokin yawon shakatawa ta lardin Jiangsu ya shedar da cewa,"Muna fatan kara samun maziyarta zuwa Jiangsu a lokacin da ake shirya bikin baje koli na duniya a Shanghai. A lokacin da suke ziyartar wurare masu ni'ima, za su iya jin dadin fahimtar al'adun gargajiya da kuma wasannin kwaikwayon gargajiya na kasar Sin. Muna maraba da dukkan jama'a, kuma mun yi imani da cewa, za su koma gida tare da samun gamsuwa matuka!"(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China