in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tsohon garin Pingle maras hayaniya da ke lardin Sichuan
2010-06-20 18:39:02 cri
Birnin Chengdu, babban birnin lardin Sichuan ya dade yana matsayin wuri mai cike da wadata a zukatan Sinawa tun can da. Yanayin wurin na da kyau ainun, kuma akwai yalwar mabambantan albarkatu masu tarin yawa. Mazauna wurin na zaune cikin kwanciyar hankali. Dimbin maziyartan da suka je Sichuan ziyara domin jin kyakkyawan sunansa kan ji dadin zaman rayuwa maras hayaniya. A dab da birnin Chengdu, akwai wasu kauyuka da garuruwa masu dogon tarihi, inda kuma mutane ka iya kara zaman diris sakamakon samun kwanciyar hankali. Yau za mu yada zango a garin Pingle mai tsawon tarihin shekaru fiye da dubu 2, da zummar kara fahimta kan al'adu na tarihi da sigar musamman ta wurin. Kafin mu fara ziyararmu a yau, zan yi muku wata tambaya, ko za ku iya rike shekaru nawa ne garin Pingle ya kwashe a doron kasa? Masu saurare, ya fi kyau ku kade kunnuwanku sosai domin amsa tambayarmu ta yau!

Garin Pingle na da nisan kilomita 93 a tsakaninsa da birnin Chengdu a kudu maso yamma. A can da an taba kiransa Pingluo, amma a shekarar 2004, an canza sunansa zuwa Pingle da fatan ganin duk wanda ya kai ziyara garin zai iya samun zaman lafiya da farin ciki, wato Ping An Kuai Le a Sinance.

Ruwa shi ne yi fitar da kyan surar garin Pingle. A lokacin da ake yawo a tsakanin tsoffin gine-gine a garin, ana iya ganin ruwa a ko ina, wannan ya kan faranta rayukan jama'a sosai. Zhu Dan, wadda ke jagorantar maziyarta ta yi karin bayani da cewa,"Titin da muke tattaki a kai yanzu shi ne titin Shuijingjie. Kuma wannan magudanar ruwa fa tsawonta ya zarce mita dari 5. An shimfida gadoji fiye da 10 a kanta, wadanda siffofinsu suka sha bamban da juna. Ana iya kara fahimtar sigar musamman da garinmu na Pingle yake da ita a wannan titi, kamar cincin iri daban daban masu dadi."

In an ambaci sigar musamman da garin Pingle ke da ita, nan take za a tuna da dogon tarihinsa. Yau shekaru dubu 2 ko fiye da suka wuce, garin Pingle ya kafu. Tituna,gidan ibada, gadoji, itatuwa, madatsar ruwa, kofofi da hanyoyi, wakoki da al'adun gargajiya masu dogon tarihi dukkansu sun kara kyautata kyan surar wannan gari.

Garin Pingle na kasancewa a bakin kogin Baimohe da ke gangarawa a duk tsawon rana da dare. A ganin mazauna wurin, wannan kogi ya yi kama da mahaifarsu. Sa'an nan, ga alama wani tsohon icen Banyan da ke dab da gada kuma a bakin kogin Baimohe, kuma yana tsaron garin ko da yaushe yana samarwa mazauna wurin kariya. Zhu Dan ta ce,"Tsawon tarihin wannan ice ya kai misalin shekaru dubu 1 da dari 5. Ya zuwa yanzu yana ci gaba da rayuwa, don haka wadanda ke zaune a garinmu muke ganin cewa, yana da rai, kuma yana iya kiyaye mu. Bisa wata al'adar gargajiya da ake bi a wurin, an ce, an mayar da jarirai tamkar 'ya'yan wannan ice na Banyan, ta haka icen zai kare su a duktsawon rayuwarsu. Kuma a ranar 1 ko ta 15 ta ko wane wata bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, 'yan kasuwa da yawa kan je wajen wannan ice tare da nuna masa girmamawa, da fatan samun kudi da yawa."

A garin na Pingle, dimbin jama'a sun dade suna zaune a wajen har na tsawon daruruwan shekaru, kawo yanzu suna bin hanyar zaman rayuwa da kakanin-kakaninsu suka saba bi tun can da.

Lokacin da maziyarta suke yawo a garin Pingle, suna iya gano wani shagon sayar da tsimammen waken soya da wata tsohuwa madam Chen take sarrafa shi. Daga nesa ana iya sansano kamshi ko tashin tsimammen waken soya da sauran kayayyakin kamshi irin wadanda ake samarwa a Sichuan suke samarwa. An rataye wani katako a kofar shagon, inda aka rubuta "Zui Pingle Lao Dian", wato tsohon shagon da ke sayar da abinci mafi tsantsar dandanon garin Pingle. Katakon shi ne ke bambance wannan shago da sauran shaguna. Madam Chen ta gaya mana cewa,"Katakon, lambar yabo ne da hukumar wurin ta ba ni. Na fara amfani da wadannan kayayyakin kamshi wajen dafa abinci tun lokacin da nake karama. Wannan shago na da dogon tarihi. Kana iya sayen duk abin da kake so bayan da ka dandana kadan. Ina gamsuwa da harkokin ciniki a shagona."

Wani ya nemi dandana abun da madan Chen ke sayarwa. Madam Chen ta ce,"Dandana duk abin da kake so. Wannan na da yaji. Wannan kuma na da zaki. In ba ka son yaji, wannan ya fi."

Kusan dukkan masu ziyara a garin Pingle suna sha'awar kara yawan kwanaki a garin. Da shigarsu garin, za su sheda zaman rayuwa na rashin hayaniya a nan, haka kuma, nan take sai su dan rage saurin tafiya. Madam Zhu ta ce,"Maziyarta za su iya shiga garinmu cikin sauri. Akwai ni'imtattun wurare a garinmu. Mazauna garin kuma, bayan mun gama aiki, mu kan sha shayi tare da abokai, mu yi hira."

Shan shayi da yin wasa da kati ko kuma rufe idanu domin dan hutawa kadan tare da shan iska mai ni'ima su kan faranta rayukan wadanda suka yi yawo a garin Pingle matuka.

Haka zalika kuma, cikin dare wannan tsohon gari na da kyan gani sosai. A kan kunna fitilu masu launuka daban daban a gidaje a bakunan koguna. Hasken fitilu masu launuka daban daban kan dace da kogunan da ke gangarawa ko da yaushe. A wannan lokaci kana iya farin cikin fahimtar kyan surar garin da dare, cin gasasshen abinci, da kuma saka fitilu a koguna da zummar samun alheri.

Masu saurare, in kun kai ziyara a garin na Pingle, kuma kun taki sa'a, watakila za ku iya halartar bukukuwan gargajiya masu sigar musamman daban daban da a kan shirya a garin a mabambantan lokuta. Madam Zhu Dan ta gaya mana cewa,"A yayin ko wane bikin tunawa da magabatanmu wato Qingmingjie mu kan saka fitilu a koguna, sa'an nan mu kan shirya kasaitaccen biki a ranar 11 ga watan Maris bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin. Baya ga hakan, mu kan yi murnar ranar haihuwar babban Buddha a babban tsaunin Jinhuashan a ranar 6 ga watan Yuni bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin. A lokacin zafi kuma, mu kan shirya gasar rera wakoki a kan koguna, inda mazauna wurin da maziyarta dukkansu suke iya shiga ciki domin gogawa da juna."

Tsohon garin Pingle na kusa da birnin Chengdu, kuma ana samun saukin kaiwa da kamowa a tsakanin wadannan wurare 2, bugu da kari mazauna wurin da yawa sun yi wa gidajensu kwaskwarima domin karbar baki. Wadannan kananan otel-otel na da tsabta, amma farashin dakunansu na da rahusa. Ta haka mazauna birnin Chengdu da yawa kan je garin Pingle ziyara a karshen mako domin hutawa. Mr. Hu da ke zaune a Chengdu ya gaya mana cewa, a lokacin bazara na bana, shi da iyalinsa kan je garin na Pingle a kusan dukkan karshen mako, inda ya ce,"Na kan ziyarci nan a kusan ko wane mako. Garin na kusa da Chengdu sosai. Na kan fuskanci babban matsin lamba a harkokin aiki, ta haka ina so in saki jiki da kwantar da hankali a karshen mako."

Wasu kan ce, a zuciyar ko wane mutum, kyan surar garin Pingle ta sha bamban. Wannan tsohon gari na maraba da ku domin sakin jiki.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China