A cikin wannan yanki kuma, birnin Barcelona na kasar Spaniya zai ba mu misalai 2 da zummar nuna kyan surarsa a matsayinsa na birni dake kunshe da al'adun kasa da kasa. To, yau bari mu yi hira a game da wata duniya mai kayatarwa da Barcelona ta samar mana ta hanyar amfani da madubai.
Rumfar nune-nune ta birnin Barcelona tana yankin da ake nuna yadda aka fi kyautata birane a farfajiyar gudanar da bikin. Barcelona birni ne daya tak na waje da zai nuna misalai 2 a wannan yanki, wato yin kwaskwarima kan tsohon bangaren birnin da kuma yadda ake kokarin raya birnin bisa ra'ayin kirkire-kirkire. Ignacio Anoveros mai zayyana rumfar nune-nune ta Barcelona ya yi karin bayani da cewa,"A rumfarmu, muna kiran bangaren nune-nune da sunan 'tsibiri'. Akwai tsibirai 5 a duk rumfar, wadanda suka shafi wuraren al'umma, hanyoyi, muhimman ayyuka, gidaje, hadin kan al'umma da kuma farfadowar tattalin arziki. A gefuna 2 na ko wane tsibirin, an saka madubi guda mai tsayin mita 7 da fadin mita 7, da nufin sanya maziyarta yin wani tunanin gaibu, ta haka za su kasance kamar yadda suna yin tattaki ne a Barcelona."
Kamar yadda Ignacio ya fada, a dukkan tsibiran 5 da aka gina ta yin amfani da mabambantan babban take, masu zayyana sun yi amfani da manyan fuskokin telibijin 2 wajen nuna yadda ake yin kwaskwarima kan tsohon bangaren birnin, da raya sabon bangaren. Suna nuna kyan surar birnin Barcelona na zamani kuma mai dogon tarihi ta hanya mai ban sha'awa. Amma akwai abubuwa da yawa da suka fito fili a birnin Barcelona, yaya aka yi wajen zabo wanda ya fi wakiltar wannan birni domin nuna wa kasashen duniya? Ignacio ya ba mu amsa, inda ya ce,"Babban take na zayyana rumfar nune-nune ta Barcelona shi ne madubi. Madubi, wata alama ce. Ana iya kyautata yin hangen nasa kan makoma bayan da aka waiwayi al'amuran tarihi. Dan haka mun yi shirin nuna kyan surar birnin ta hanyar yin amfani da madubai. Ana sane da cewa, Barcelona wani birni ne inda al'ummomi daban daban suke rayuwa tare, kuma al'adu iri-iri sun hadu a wajen. Muna fatan ta hanyar amfani da madubai da dama, za a iya bayyana wa mutane cewa, 'Barcelona wani birni ne mai kunshe da al'adun kasa da kasa'."
Mene ne alamar Barcelona da ta fi jawo hankali? Ba shakka, Antonio Gaudi, wani fitaccen mai aikin zayyana da kuma shahararrun gine-ginen da ya zayyana! Ciki kuma, mutum-mutumin da Gaudi ya kera da tayil-tayil masu launuka daban daban a lambun shan iska na Guell ya fi jawo hankalin kasashen duniya. Ana kiransa Dodon Gaudi, wato "Dragon of Gaudi" ta bakin Turawa, ko kuma Gao Di Long ta bakin Sinanci. Da zummar yin maraba da bikin baje koli na duniya da za a yi a Shanghai, hukumar Barcelona ta kwaikwayi saka wannan alamar birnin, ta ba wa kasar Sin abun kwaikwayar tamkar wani abun kyauta. Wannan abun kwaikwayar da girmansa da siffarsa suka yi daidai da Gao Di Long ba zai bar kasar Sin ba har abada. Game da wannan, Ferran Ferrer, shugaban rumfar nune-nunen Barcelona ya gaya mana cewa,"Dalilin da ya sa muka zabi Gao Di Long bai wuce cewar shi ne alamar birnin Barcelona ta fannonin gine-gine da kuma yadda ake kokarin raya birnin ta hanyar zamani. Littattafan Sinanci da yawa sun saka shi a bangwayensu, ta haka muna iya gano cewa, ya shiga zukatun mutane sosai. Baya ga hakan kuma, dabbar Long, wani muhimmin bangare ne na al'adun gargajiya na kasar Sin, kuma wata alamar shekara ce ga al'adun Sinawa. Muna fatan dabbar Long da ta fito daga Barcelona za ta kawo wa Sinawa alheri. Saboda haka, mun ba wa magajin gari na birnin Shanghai Gao Di Long tamkar abun kyauta da zummar kawo wa Shanghai alheri."
Baya ga wannan mutum-mutumi mai ban sha'awa, a matsayinta na babban birni mai muhimmanci, Barcelona ta koya mana darasi kan yadda ake tsara shiri kan birane da kuma bunkasa su ta hanyar da ta dace. Ferran Ferrer ya yi mana karin bayani kan kyakkyawan sakamakon da wannan birnin da ke bakin tashar jiragen ruwa ya samu wajen raya kansa, inda ya ce,"A daidai lokacin da muka samu damar shirya gasar wasannin Olympic a karo na 25, wato a shekarar 1986, mun gabatar da shirin yin amfani da damar shirya gasar domin sauya hanyar bunkasa birnin tun daga tushe. Ta haka mun gano wata sabuwar hanyar tsara shiri kan raya birane sannu a hankali. A maimakon lalata tsohon bangaren birnin, mun gina sabon bangaren kasuwanci a birnin. Kuma muna kokarin sanya dukkan bangarorin 2 don su hadu sosai, ta haka muna iya samar da isassun gidajen kwana, ofisoshi da kuma raya masana'antu a lokaci guda ta hanyar da ke dacewa. Ta bin irin wannan hanya ne muke iya kare al'adun gargajiya na Barcelona, hatta ma muna iya kyautata rawar da Barcelone ke takawa a matsayinta na birni na zamani,haka zalika, mun fito da kyakkyawan sakamako na raya Barcelona a nan gaba da kuma bunkasa sauran biranen duniya."
A sakamakon kara sanin sashen Barcelona, abin da ya sa ba ma kawai muna iya fahimtar karfin birnin na samun bunkasa ba, har ma muna iya kara fahimtar babban taken bikin baje koli na duniya da za a yi a Shanghai, wato "birane masu kayatarwa, kuma zaman rayuwa mai dadi". Ferran Ferrer yana darajta wannan babban taken sosai. A ganinsa, wannan na da muhimmiyar ma'ana wajen bunkasa duniya. Yana mai cewa,"Wannan babban take ya nuna ainihin burin kasar Sin na shirya bikin baje koli na duniya. Yanzu mutanen da yawansu ya wuce rabin jimillar mutanen duniya suna zaune a birane, ta haka ya kamata mu mai da hankali kan yadda za mu ji dadin zaman rayuwa a birane. Babban taken na bikin baje koli na duniya da za a yi a Shanghai ya kara jaddada mana muhimmancin birane a zaman rayuwarmu. Sa'an nan kuma, a cikin watanni 6 masu zuwa, za mu yin kokarin yada halayyar Barcelona a nan kasar Sin, za mu yi wa mutanen Sin da masana'antun kasar karin bayani kan tattalin arzikin birninmu mai ci gaba da kyakkyawan yanayi ta fuskar raya kasuwanci da zummar jawo karin maziyarta zuwa birninmu. Haka kuma, za mu karfafa gwiwar karin masana'antun Sin da su zuba jari a Barcelona da nufin aza harsashi mai kyau ta fannin yin hadin gwiwa a tsakanin bangarorin 2 a harkokin kasuwanci, tattalin arziki da kuma ciniki."(Tasallah)