in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ina dalilin da ya sa rumfunan nune-nune
2010-06-20 18:35:13 cri
Bayan da aka bude bikin baje kolin duniya na EXPO a birnin Shanghai a gabashin kasar Sin a ran 1 ga watan Mayu, rumfunan nune-nune guda 10 kamar na kasar Sin, na birane da lardunan kasar Sin, na yayata babban taken bikin, na kasashen Switzerland, Faransa, Jamus, Belgium, Saudiya da Korea ta Kudu sun fi karbar dimbin maziyarta a farfajiyar. Masu saurare, yau ma Garba da ni za mu yi kokarin bayyana sirrinsu na jawo hankalin maziyarta!

Kafin an shiga cikin rumfar Korea ta Kudu, ana iya jin kide-kiden kasar. Masu fasaha daga Korea ta Kudu su kan nuna wasanni 12 a ko wace rana a dandamalin da ke kasan bene na farko a rumfar, wadanda suka hada da raye-raye da kide-kiden gargajiya. A wasu lokutan musamman kuma, taurarin fim da shahararrun mawakan Korea ta Kudu su kan bayyana a rumfar domin jawo karin maziyarta, a kokarin nuna wa kasashen duniya kyan fasalin Korea ta Kudu ta hanyar bikin EXPO na Shanghai. Matasan kasar Sin da yawa suna Alla-Alla wajen kai ziyara a rumfar. Fu Ying, wata kyakkyawar budurwa ta gaya mana cewa,"Siffar wannan rumfa ta jawo hankalina sosai. Ina son in kara fahimtarta. Korea ta Kudu da Sin, kasashe ne na Asiya. Al'adunsu sun yi kama da juna. Na koyi abubuwa da yawa a rumfar. Kuma na ga wasu shahararrun mawakan da muka san su a lokacin da muke kanana."

A hakika, a tarihin Korea ta Kudu na halartar bikin EXPO, rumfar da ta kafa a birnin Shanghai ta fi girma. Korea ta Kudu tana fatan ta hanyar shiga bikin EXPO na Shanghai, rumfarta za ta taka rawa sosai a matsayin jakadiyar kasa. Kim Joon Ki, darektan rumfar Korea ta Kudu ya fadi cewa,"A lokacin da maziyarta suke jiran shiga rumfarmu, suna iya yin yawo ba tare da gamuwa da wani shinge ba. Mu kan bude duk rumfarmu gare su. Sa'an nan in aka tsaya a wurare daban daban a wajen rumfarmu domin daukar hotuna, to, hotunan da aka dauka kan sha bamban da juna. Ba kawai muna yin karin bayani kan fasahohi a rumfarmu ba, hatta ma muna sa muhimmanci kan yayata al'adu, musamman ma muna mai da hankali kan yin mu'amalar abokantaka da kasar Sin. A rumfarmu, maziyarta suna iya zazzagayawa tare da yin wasa."

Bayan fita daga rumfar Korea ta Kudu, ana iya kara kokarin fahimtar rumfunan kasashen Turai, wadanda wasu daga cikinsu suka fi samun karbuwa sosai. Maziyarta kan yi mamaki bisa ganin wadannan rumfuna masu ban sha'awa.

Rumfar Jamus ita ce rumfar kasar waje da ta fi karbar dimbin maziyarta. A lokacin da ake gwajin tafiyar da ita, an rufe kofarta kafin lokacin da aka tsara saboda yawan maziyarta fiye da kima a rana ta farko. A farkon wannan wata kuma, a ko wace rana ana iya ganin jerin gwano na mutane a kofar wannan rumfa. Wakilinmu ya tambayi Peter Kreutzberger, mataimakin babban wakilin Jamus mai kula da harkokin nune-nune a bikin EXPO na Shanghai kan yadda ake iya shiga rumfar Jamus cikin sauri. A ganin Kreutzberger, ba dabara! Amma ya yi farin ciki matuka da ganin maziyarta masu yawa haka a rumfar Jamus, inda ya ce,"Mutane sun san wasanninmu. A rumfunan da na taba ziyarta zuwa yanzu, akwai fina-finai, amma ba wasanni. Sa'an nan a wasu rumfuna, kuna iya yin ziyara amma ba ku iya shiga cikin wasu harkoki. A rumfarmu, maziyarta suna iya shiga wasu harkoki masu ban sha'awa, musamman ma yara suna son ziyarar rumfarmu. Ba shakka dalilin da ya sa haka shi ne domin Sinawa sun dan san Jamus, in an kwatanta da wasu kasashen Turai da ba su taba jin sunayensu ba. Ta haka su kan je rumfarmu ta Jamus ziyara."

Kasashe da yawa suna nuna fasahohin zamani a rumfunansu, yayin da suke kokarin yayata al'adunsu. Wasu kasashe sun je birnin Shanghai da dukiyoyin kasa masu daraja, kamar zane-zane da mutum-mutumi da fitattun masu zane-zane da masu sassaka na Faransa suka yi su. A cikin jerin gwanon da ke jiran shiga rumfar Faransa, da yawa daga cikinsu sun dauki tsawon lokaci suna jira. Madam Xiang da ta bin layi ta gaya mana cewa,"Na iso farfajiyar da karfe 7 na safe. A rumfar Faransa, akwai dukiyoyin kasa guda 7 masu daraja. A lokacin da na kai ziyara a Faransa, ban samu damar kallonsu ba gaba daya, kuma ana bukatar yin rajista, yin jerin gwano da tsawon lokacin jira. Amma a farfajiyar, bayan awoyi 2 kawai, na iya kallonsu duka, wannan yana da kyau matuka. Yawancin maziyarta ba su da damar zuwa Faransa."

A farfajiyar bikin, rumfar kasar Sin tana da matukar kayatarwa! A hakika ban da rumfar kasar Sin, rumfar larduna da biranen kasar Sin ita ma ta samu karbuwa sosai a gurin baki, kamar ni. Sinawa su kan ziyarce su da zummar kara sanin bunkasuwar kasarsu, baki kuma kan ziyarce su ne da nufin kara fahimtar kasar Sin. Mr. White, wani maziyarci ne daga kasar Holland ya fada mana cewa, fim din da wani mai hada hotunan fina-finai na kasar Sin ya dauka a game da bunkasuwar kasar Sin ta tsawon shekaru 30 ya burge shi sosai. Yana mai cewar,"Fim din na da ban sha'awa, inda na kara ilmi kan hanyar da kasar Sin ta bi, a kokarin samun bunkasuwa. Mutane na sassa daban daban na duniya suna kokarin kyautata zaman rayuwarsu, haka ma Sinawa. A hakika, hawaye ya kusan fitowa daga idona. Kasar Sin ta dauki tsawon lokaci tana himmantuwa wajen samun wadata da bunkasuwa da kyautata zaman rayuwar jama'a. A ganina, ina da alhakin kara sanin abubuwan da kasar Sin take son gaya wa duniya ta hanyar shirya bikin EXPO na Shanghai."

Rumfar birane da lardunan kasar Sin za ta taimaka sosai, inda larduna da birane da jihohi 31 na kasar Sin suke nuna fasaha da sigar musamman da suke da ita ta hanya mai dacewa. Mr. Kent, wani dan Amurka bayan da ya ziyarci rumfar birane da lardunan kasar Sin, ya ce,"Ina sha'awar wannan rumfa kwarai da gaske. Ina matukar sha'awar zazzagayawa kasar Sin. Rumfar kamar ta samar mana da shawarwari a game da wuraren da zan kai ziyara. Bayan na gama ziyartar dakin nune-nune na lardin Gansu, sai na fahimci wurin da zan kai ziyara."(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China