Wan ya kara da cewa, babban taken bikin EXPO na Shanghai, wato "birni mai kayatarwa da kuma zaman rayuwa mai inganci" a karo na farko hakika ya nuna yadda bunkasuwar birane ke kara taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban 'yan Adam. Sabunta kimiyya da fasaha zai tabbatar da yin jagoranci kan yadda za a raya birane a nan gaba, inda za a fi yin amfani da tsabtaccen makamashi a birane, tare da kyautata amfani da albarkatu yadda ya kamata wajen raya tattalin arzikin birane, sa'an nan za a tafiyar da harkokin birane ta hanyar da ta dace, sana'ar ba da hidima da ke bukatar ilmi sosai za ta kasance wani ginshiki ga birane, har wa yau kuma, za a kara samun jerin birane a nan kasar Sin.
Mr. Wan ya ci gaba da cewa, kasar Sin za ta kara karfin sabunta kimiyya da fasaha, da raya sabbin sana'o'i, da kara raya birane don su dace da zaman rayuwa kuma masu jituwa. (Tasallah)