in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana mai da hankali kan sauyin farashin amfanin gona a kasar Sin
2010-06-18 21:04:08 cri
Ibrahim: A cikin 'yan watannin da suka gabata, farashin tafarnuwa da kayayyakin lambu da koren wake da masara dukkansu sun karu. Sakamakon haka, jama'a sun nuna damuwa kan raguwar darajar kudi. Wasu jami'ai wadanda suke sa ido kan harkokin tattalin arziki sun bayyana cewa, dalilin da ya sa hakan shi ne an samu sauyi a kasuwa sakamakon sauyin yanayi na duniya. Sannan, mai yiyuwa ne wasu mutane sun zuba dimbin kudade kan amfanin gona domin yunkurin samun karin riba. Amma galibin masana sun bayyana cewa, hauhawar farashin wasu kayan amfanin gona ba za ta yi tasiri ga sauran kayan amfanin gona ba.

Sanusi: Jama'a masu sauraro, yanzu ne lokacin da aka soma girbin tafarnuwa a kasar Sin. A gundumar Zhongmo, wato "garin tafarnuwa" dake lardin Henan, 'yan kasuwa sun riga sun yi odar kusan dukkan tafarnuwar da har yanzu ba a girbe su ba tukuna a gundumar. An bayyana cewa, farashin tafarnuwar da aka yi jigilarsu daga gundumar Zhongmo zuwa birnin Zhenzhou, babban birnin lardin Henan ya kai kudin Sin yuan dubu 8 ga kowane ton daya, wato kwatankwacin kudin Sin yuan 8 ga kowane kilo. Amma a shekarar 2008, farashin tafarnuwa ya kai kudin Sin yuan 0.1 kawai ga kowane kilo. Madam Li Zhixia wadda ta yi shekaru 30 ko fiye tana noman tafarnuwa ta ce, ta yi mamakin yadda farashin tafarnuwa ya yi tashin gauron zabo fiye da kima, inda ta bayyana cewa, "Na ga farashin tafarnuwa ya fi tsada a bana. A 'yan shekarun baya, farashin tafarnuwa ya kai kudin Sin yuan 0.1 ga kowane kilo, mun samu kudin da yawansa ya kai kudin Sin yuan dubu 3 kawai daga kowace hekta, wadannan kudade ba su kai yawan kudin da muka kashe wajen noman su ba, balle albashin 'yan kwadago da riba. Amma farashin tafarnuwa a bana ba yabo ba fallasa, ba mu taba ganin irin wannan al'amari a baya ba."

Ibrahim: Ban da tafarnuwa, bayan an shiga lokacin zafi, jama'ar kasar Sin za su soma cin koren wake domin yakar zafi. Sakamakon haka, farashin koren wake ya karu. A lardin Heilongjiang da ke arewa maso gabashin kasar Sin, wato muhimmin lardi ne da ke samar da koren wake, shi ma farashinsa wake ya kai kudin Sin yuan 18 daga yuan 4 kan kowane kilo. Madam Zhou wadda ke cinikin amfanin gona a lardin ta ce, "Haka ne. Farashin koren wake ya hau daga yuan 2 zuwa yuan 18 ga kowane kilo, a kan karu da yuan 1 ko rabin yuan a kowane karo, farashin yana karuwa cikin sauri sosai."

Sanusi: Kamar yadda farashin tafarnuwa da na koren wake suke karuwa cikin sauri, farashin masara ma ya karu cikin sauri. Bisa kididdigar da aka yi, an ce, farashin masara ya kai kudin Sin yuan dubu 2 a kasuwa yanzu daga yuan dubu 1 da dari 8 a watan Maris. A gundumar Jiutai ta lardin Jilin, manomi Xu Jun wanda ke noman masara ya ce, yanzu farashin masara yana karuwa cikin sauri.

"Farashin masara ya karu, wato ya kai kudin Sin yuan 1.64 yanzu daga yuan 1.08 ga kowane kilo. Farashin masara ya yi wata 1 ko fiye da karuwa."

Ibrahim: Lokacin da take bayyana dalilin da ya sa hauhawar farashin wasu kayan amfanin gona, madam Ma Shuping, mataimakiyar direktan hukumar shuke-shuke ta ma'aikatar aikin gona ta bayyana cewa, yawan gonakin da aka noma nau'in wasu kayayyakin lambu ya ragu a bara. Sakamakon haka, yawan amfanin gona da ake samarwa a kasuwa ya ragu a bana, amma yawansu da masu sayayya suke bukata yana ta karuwa. Wannan ne muhimmin dalilin da ya sa farashinsu ya karu.

"Yawan gonakin da aka noma koren wake ya ragu a bara, amma yawan amfanin gona da aka fitar zuwa kasashen waje ya karu, sannan yawan wadanda ake shigowa daga kasashen waje ya ragu. Sabo da haka, yawan koren wake da ake samarwa a kasuwar gida ya ragu. Sakamakon haka, farashin koren wake ya karu. Bugu da kari, yawan tafarnuwa da aka samar ya kai ton miliyan 12 a shekarar 2009, wato ya ragu da ton miliyan 6 bisa na shekarar 2008. Wannan ne babban dalilin da ya sa farashin tafarnuwa ya karu a bana."

Sanusi: Bugu da kari, Mr. Li Guoxiang, wanda ke nazarin batutuwan da suka shafi bunkasa yankunan karkara a kasar Sin yana ganin cewa, farashin amfanin gona ya samu sauye-sauye ne domin wasu mutane sun zuba karin jari a kasuwar cinikin amfanin gona. Mr. Li ya bayyana cewa, "Ko da yake masu zuba jari ba su iya sarrafa kasuwar amfanin gona sosai ba, amma yanzu sabo da sun yi amfani da sauyin da ke kasancewa a tsakanin yawan amfanin gona da ake bukata da yawansu da aka samar a kasuwa, irin wannan sauyi ya kara tsananta."

Ibrahim: Amma, jama'a masu sauraro, bayan da gwamnatin kasar Sin ta dauki jerin matakai, kuma yanzu an soma shiga lokacin zafi, farashin yawancin amfanin gona ya soma raguwa. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China