in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi bikin murnar ranar dakin kasar Seychelles a farfajiyar bikin baje koli a Shanghai
2010-06-18 14:41:53 cri

Ranar 18 ga wata ranar dakin kasar Seychelles na bikin baje kolin duniya a Shanghai, jakadan Seychelles dake kasar Sin kana wakilin dakin kasar Mr Philippe Le Gall da kuma mataimakin babban wakilin gwamnatin kasar Sin mai kula da harkokin bikin baje koli Mr Jiang Zhengyun sun halarci bikin murnar.

Gall ya yi jawabin nuna godiya ga goyon baya da jama'ar Sin suke nuna wa dakin kasarsa. Kuma ya ce, taken dakin kasar shi ne "Misalin Seychelles na bunkasa birane cikin dogon lokaci", wanda ya bayyana yadda ake bunkasa tattalin arziki da al'umma da muhalli baki daya.

Gall ya ce, yana fatan fasahohin Seychelles zasu zama wasu abubuwa masu daraja ga bikin baje koli na Shanghai, kuma zai ba da gudunmawa wajen mai da babban taken bikin baje koli na Shanghai da ya zama wata ka'ida domin kiyaye muhalli.(Amina)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China