Elisabeth Tankeu, wakiliyar kula da harkokin ciniki da masana'antu ta kwamitin tarayyar Afirka, ta ce, biranen Afirka na bunkasa cikin sauri, ba za a iya daidaita matsalar gibin da ke tsakanin masu arziki da matalauta da kuma rashin kwanciyar hankalin al'umma ba, illa sai an kula da biranen yadda ya kamata, ta ce,"Muna sa ran kwamitin tarayyar Afirka da mambobin tarayyar Afirka za su samu wata sabuwar hanyar tabbatar da zaman lafiya da tsaro bisa ga halartar bikin baje kolin duniya da ake yi a Shanghai." (Lubabatu)