Babban wakilin dakin kasar Namibia dake bikin EXPO na Shanghai H.P Asheeke ya ce, kasar Namibia ta dora muhimmanci sosai kan bikin EXPO na Shanghai, tana fatan mutanen duniya za su kara fahimtarta. H.P Asheeke ya ce, "Mun yi niyyar shiga bikin EXPO na Shanghai, sabo da mun yi tsammani cewa, hakan zai shaida dankon zumuncin dake tsakanin kasashen Sin da Namibia. A sa'i daya kuma, muna fatan za mu kara yin musayar ra'ayi tare da jama'ar kasar Sin da ta sauran kasashen duniya a fannonin neman samun bunkasuwa da tinkarar kalubale."
A cikin dakin nune-nune na kasar Namibia, an iya ganin kayayyaki masu ban sha'awa da itattuwan musamman na wannan kasa.