in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gudanar da ayyukan bikin baje kolin duniya cikin lafiya a watan farko da ake shirya bikin
2010-06-01 18:03:49 cri

Yau wata daya ke nan da aka fara gudanar da bikin baje kolin duniya na shekarar 2010 a birnin Shanghai da ke gabashin kasar Sin. A ran nan, Mista Hong Hao, mataimakin babban sakataren gwamnatin birnin Shanghai, kuma shugaban hukuma mai kula da bikin EXPO, ya kira wani taron manema labaru a cikin farfajiyar bikin EXPO, inda ya bayyana halin da ake ciki wajen gudanar da ayyuka daban daban na bikin EXPO, kamar yadda ya fadi cewa, an gudanar da ayyukan cikin koshin lafiya, dukkan ayyukan da suka shafi tsaro, da karbar baki, da tsabtata muhalli, da ingancin abinci, da kuma bukukuwan da aka shirya, an kula da su yadda ya kamata. Sa'an nan Mista Hong ya ce a watan Mayu kadai an samu mutane fiye da miliyan 8 wadanda suka kai ziyara a farfajiyar bikin EXPO, har ma an taba karbar baki fiye da dubu 500 a rana guda. Duk da cewa ana fuskantar kwararowar baki masu yawan gaske, amma hukuma mai kula da aikin shirya bikin baje kolin duniya ta samar da tabbaci a fannin hidima, kamar yadda Mista Hong ya fadi cewa, 'Bayan budewar farfajiyar bikin EXPO, mun kara sanya wasu allunan bayyanai na lantarki 57 a cikin farfajiyar da kuma a wajen kofofi, sa'an nan mun kara laimomin kare hasken rana 2000, da kujeru dubu 40, da kuma kafa rumfunan hutawa a gaban dakunan nune-nunen da aka fi yawan samun masu yawon shakatawa. Haka kuma, mun sanya na'urorin fesa ruwa domin kau da zafi ga jama'a, da kuma shimfida wasu cibiyoyin ba da jinyya.'
1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China