in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban taken "ranar rumfar kasar Mali" na jaddada huldar da ke tsakanin kasashen Mali da Sin
2010-06-01 15:42:58 cri

Ran 31 ga watan Mayu, litinin da ta gabata, rana ce ta rumfar jamhuriyyar kasar Mali a yayin bikin baje koli na duniya na Shanghai, a wannan rana, an yi biki a cibiyar farfajiyar bikin EXPO na Shanghai domin murnar ranar rumfar kasar Mali. Wasannin kide-kiden da raye-raye da aka yi na irin gargajiya na Afirka sun sami maraba sosai daga masu yawon shakatawa na kasar Sin, hakan kuma jama'ar kasashen Mali da Sin sun kara yin musaya da fahimtar juna.

Amon kida mai dadin ji da sa kuzari ya fito daga cibiyar farfajiyar bikin EXPO na Shanghai inda ake yin bikin murnar ranar rumfar kasar Mali, wannan ya kasance abin kyauta mai daraja sosai da wata mashahuriyyar kungiyar wasannin kide-kide mai suna "Neba Solo" ta kasar Mali ta yi ga masu yawon shakatawa. Kungiyar wasannin kide-kide na "Neba Solo" ta kunshi maza 7 da mace 1, wakokinsu da salon kida da suka yi da ganga da sauran kayayyakin kida sun nuna amo mai kuzari sosai, wannan ya jawo hankalin dukkan mutanen da ke wurin.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China