in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bikin EXPO na Shanghai shi ne wani gagarumin shagali na duniya
2010-05-28 16:43:11 cri
Za a gudanar da bikin nune-nune cikin tsawon watanni shida, kasashe da kungiyoyi sama da 240 suka shiga bikin, kuma ana sa ran cewa yawan mutanen da za su ziyarci bikin zai kai miliyan 70. Mene ne abin da bikin EXPO na Shanghai zai kawo wa duniya? Game da wannan tambaya, mutane daban daban za su ba da amsa iri daban, amma a ganin Irina Bokova, babbar daraktar hukumar UNESCO, bikin EXPO shi ne wani gagarumin shagali ga duniya baki daya.

A ran 16 ga wata, madam Bokova ta zo kasar Sin don halartar aikacen da hukumar UNESCO ta shirya a yayin bikin EXPO. Kafin ta zo kasar Sin, Bokova ta gaya wa manema labaru na kamfanin dillancin labaru na Xinhua cewa, ba kawai bikin EXPO na da muhimmanci ga kasar Sin ba, hatta ma yana da ma'ana ga duk duniya. Ta ce, " bikin EXPO shi ne wani gagarumin shagali ga duniya baki daya, ina kai godiya ga gwamnatin kasar Sin domin ta yi iyakacin kokarin shirya bikin."

Madam Bokova ta ce, "Na ziyarci birnin Shanghai a shekarar bara, sabo da haka, na san wasu abubuwa na shirin bikin EXPO. Yanzu na iya ganin bikin EXPO, ina farin ciki kwarai da gaske. Bikin EXPO ya samar da dama ga mutane wajen yin mu'amala da tattaunawa."

Yayin da ake tabo magana kan babban taken bikin EXPO wato "Birni mai kayatarwa da zaman rayuwa mai inganci", madam Bokova ta ce, a halin yanzu, yawan mutanen dake zama a birane ya kai kashi 60 cikin dari, kuma yawansa yana karuwa. An yi hasashe cewa, a cikin shekaru 50 masu zuwa, yawan mutanen da za su zama a birane zai kai kashi 80 cikin dari. Madam tana ganin cewa, kamata ya yi kowace kasa da kungiya ta ba da gudummawa ga duniya, kuma ya kamata hukumar UNESCO ta yi haka.

Lokacin da ake hira kan ma'anar bikin EXPO ga duniya, madam ta ce, "Da farko, kasar Sin za ta bayyana karfinta. Muna iya cewa, kasar Sin ta riga ta cimma wannan buri, domin mun ga ire-iren kokarinta a kowane fanni. Ban da haka kuma, nasarar da Sin ta samu ta gaya wa duk duniya cewa, wata kasa, idan tana da makasudinta, kuma jama'arta sun rika yin iyakacin kokarin aiki, to, za ta tinkari ire-iren matsaloli."

Madam Bokova ta gabatar da cewa, muhimmin aiki na hukumar UNESCO a gun bikin shi ne aikin wayar da kai a fannin al'adu. A yayin bikin, hukumar za ta bayar da rahoto game da ire-iren al'adu, kuma za ta nuna ayyukan da ta yi wajen kiyaye kayayyakin gargajiya da aka gado daga kaka da kakani.

Madam Bokova ta furta cewa, a matsayin wata hukuma mai ba da jagoranci a fannin ba da ilimi ta M.D.D., hukumar tana dukufa kan sa kaimi wajen ba da ilimi ga dukkan jama'a. Sabo da haka, a lokacin bikin, za mu gabatar da babban ci gaba da aka samu wajen ba da ilimi mai inganci da kuma ba da ilimi ga diya mata a duk duniya. Ban da haka kuma, muna fatan yin amfani da damar bikin don tattaunawa da jama'a a kan batutuwan dake jawo hankulan jama'a kamar su sauyawar yanayi da harkokin kula da ruwa da dai sauransu.(Asabe)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China