in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Karo na farko da Nillah ta gane ma idanunta da bikin EXPO
2010-05-26 17:17:46 cri

An bude farfajiyar bikin baje kolin duniya na EXPO a birnin Shanghai da ke gabashin kasar Sin a ranar 1 ga watan Mayu, sa'an nan zuwa ranar 23 ga wata, farfajiyar ta riga ta karbi masu yawon bude ido, Sinawa da mutanen kasashen ketare, wadanda yawansu ya wuce miliyan 5. Kokarin aiki da ma'aikata masu shirya bikin suka yi ya sa mutane da yawa suka samun damar gane ma idanunsu yadda bikin baje kolin duniya yake a karo na farko, kamar yadda wakiliyar CRI Nillah take can, wadda ta zo daga kasar Kenya, sa'an nan bikin da ke gudana a Shanghai ya kasance bikin baje kolin duniya na farko da ta taba kai ziyara. Nillah ta ce, 'Yanzu na san mene ne bikin baje kolin duniya. Abubuwan da na gani a Shanghai sun burge ni sosai, ba zan iya mantawa da su ba. Da farko dai, kasashe daban daban sun gwada zane-zane da sabbin ra'ayoyi a cikin rumfunansu, abubuwan da suka ba mu damar ganin tunani mai kyau na jama'ar kasashe daban daban, wadanda suke kokarin kara samar da kayatarwa a cikin farfajiyar bikin baje kolin duniya. Ban da haka kuma, ko wace rumfa da ke madadin wata kasa na da halin musamman da abubuwa masu ban sha'awa na kanta, sa'an nan abubuwan da ake bajen kolinsu a wajen rumfar su kan dace da babban taken bikin EXPO na 'birni mai kayatarwa da zaman rayuwa mai ingaci.''
1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China