Dakin nune-nunen kasar Mozambique yana cikin rumfar nune-nune ta hadin gwiwar kasashen Afirka. Da zarar an shiga dakin, za a iya sheda burgewa sosai sakamakon kyan yankunan karkara da al'adun da ke da halin musamman na kasar Mozambique ke da shi. Bambancin da dakin nune-nune na kasar yake da shi da sauran dakuna shi ne ana iya samun yankunan nune-nune hudu a wurin a maimakon dakin nune-nune guda kawai, wadanda suka hada da wata makaranta, da wani karamin dakin kwana na gargajiya, da wani dakin kwana na zamani, kana da wani asibiti. Kogin Zambezi shi ne ya hada su tare.