in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shigarmu rumfar kasashen Afirka da ke farfajiyar bikin EXPO na Shanghai
2010-05-13 18:48:56 cri
A wajen farfajiyar inda ake gudanar da bikin baje kolin duniya na EXPO na birnin Shanghai, akwai wata babbar rumfa, wadda ta fi girma daga cikin rumfunan da kasashe daban daban suka kafa a cikin wannan farfajiyar don baje kayayyakinsu, abin da ya sa rumfar ta zama daya daga cikin rumfunan da suka fi daukar hankalin jama'a masu yawon shakatawa. An ce, rumfar ta zama tamkar wani babban akwatin zuba kaya, akwatin da aka yi amfani da shi don kwashe al'adu masu ban sha'awa da salon zaman rayuwa na musamman na jama'ar kasashen Afirka zuwa birnin Shanghai, inda za su samu damar baje wa mutanen kasashe daban daban kayayyaki daban daban.

Da zarar aka shiga cikin babbar rumfar kasashen Afirka, za a ga wasu manyan fuskokin mutanen da aka sassaka su da dutse, fuskokin da ake kiransu 'murmushin iri na Afirka'. Sa'an nan fuskar da ta fi girma, an sanya mata sunan 'Lucy'. Chen Jingtian, jami'in da yake kula da aikin tsara baje koli a cikin rumfar kasashen Afirka, ya yi mana karin bayanin cewa,

'An tsara fuskar ne bisa kwaikwayon gyauron jikin mace ta farko da aka gano a wajen inda kasar Habasha take yanzu yau da shekaru miliyan 3 da suka wuce, mutumiyar da ake kiranta Lucy, wadda ta kasance daya daga cikin kaka da kakanin dukkanin bil Adama.'

An ce, shiga cikin rumfar kasashen Afirka da ke farfajiyar bikin EXPO na Shanghai, zai kasance kamar shiga wani wurin da aka dunkule dukkan abubuwan da za a iya samu a nahiyar Afirka, domin a wajen ne aka nuna wa masu yawon bude ido tarihi da al'adun musamman na kasashe 42 da ke nahiyar Afirka.

Kasar Botswana ta kasance daya daga cikin kasashen Afirka wadanda suka yi fice wajen raya tattalin arzikinsu, domin yawan albarkatun lu'u-lu'un da kasar ke da shi da yawan lu'u-lu'un da take sayarwa suna kan gaba a duniya. Saboda haka, kasar ta fi mai da hankali kan baje albarkatun dabbobi da na itatuwa da take da su, da kuma gwada yadda ake haka lu'u-lu'u daga karkashin kasa.

Sa'an nan, kasar Zimbabwe ta fi dora muhimmanci kan nuna tsoffin biranen da kaka da kakanin mutahen kasar suka gina, abubuwan da suka ba jama'ar kasar yin alfahari sosai, har ma sun sanya zanen biranen kan tutar da tambarin kasar, kamar yadda Yu Chenlu, ma'aikaciyar da ke aiki a cikin babbar rumfar kasashen Afirka, ta bayyana mana cewa,

'Zimbabwe ta shahara a duniya sakamakon tsoffin biranen dutse na kasar, shi ya sa aka gina rumfar kasar Zimbabwe da duwatsu, inda takanas ne aka yi zanen kwaikwayon siffar tarkacen wani tsohon gari mai taken David, wanda ya fi shahara, lokacin da aka yi kokarin tsara rumfar kasar.'

Cikin babbar rumfar kasashen Afirka, an shimfida kananan rumfuna fiye da 40 domin kasashe daban daban da ke nahiyar Afirka, da kuma kungiyar kawancen kasashen Afirka ta AU, su baje kayayyakinsu. Ban da haka kuma, an kafa babban dandalin inda za a shirya nune-nunen fasaha, da kuma manyan kasuwanni 2 da suka kasance a karshen rumfar wato daga gabacinta da kuma yammacinta. Sa'an nan, Chen Furong, darekta mai kula da rumfar kasashen Afirka, ta gaya mun cewa,

"An hada wuraren da kasashe daban daban za su yi amfani da su don sayar da kaya a waje daya, ta yadda aka kafa kasuwanin gabas da yamma. Abubuwan da ake sayarwa an kawo su ne daga kasashen Afirka da ke da nisa da kasarmu sosai. Sun kasance kayayyakin aikin hannu irin daban daban."(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China