in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bikin baje koli na duniya na Shanghai ya ba da hidima ga masu yawon shakatawa daga dukkan fannoni
2010-05-13 16:40:33 cri
Ya zuwa yau, an gudanar da bikin baje koli na duniya na Shanghai cikin tsawon kwanaki 13. Game da matsalolin da suka bullo, bangarori daban daban sun daidaita shiye-shirye cikin lokaci kamar yin hasashe kan yanayi, da tafiye-tafiye da kuma halin cin abinci don ba da hidima ga masu yawon shakatawa.

A lokacin da ake tafiyar da bikin Expo, za a fuskanci wasu ire-iren yanayi maras kyau da za su kawo illa ga masu yawon shakatawa da kuma yadda ake tafiyar bikin. Game da haka, Zheng Guoguang, shugaban hukumar yin hasashe kan yanayi ta kasar Sin ya bayyana cewa, don ba da hidima mafi kyau ga masu yawon shakatawa, hukumar za ta yi amfani da fasahohi na zamani wajen sa ido kan yanayi, kuma za ta yi hasashe kan yanayi ga masu yawon shakatawa ta hanyoyi daban daban.

"Mun mai da hankali kan kafa wani tsarin sa ido kan yanayi a shiyyar bikin Expo da yankunan dake kewayenta. Za mu yi hasashe kan yanayi a kowace awa a shiyyar Expo, kuma za mu sanar da masu yawon shakatawa ta hanyoyi shida a cikin mintoci 15."

Ban da hukumar yin hasashe kan yanayi, hukumomin tafiye-tafiye na birnin Shanghai sun tsara shiri game da tafiye-tafiye. Masu yawon shakatawa suna iya shiga shiyyar Expo ta hanyoyin jiragen kasa da bas da motoci da kuma jiragen ruwa da dai sauransu. Bisa bincikin da bangare mai shirya bikin ya yi, an ce, tun lokacin bude bikin zuwa ran 11 ga wata da dare, yawan mutanen da suka shiga shiyyar ya zarce miliyan daya da dubu 740. Ana fi son sayen tikitoci a wurin da sayen tikitocin ziyara shiyyar da dare.

Sun Jianping, shugaban kula da harkokin tafiye-tafiye a tashoshin jiragen ruwa na birnin Shanghai ya tabbatar da cewa, hukumomin kula da harkokin tafiye-tafiye za su yi la'akari kan ire-iren kalubalen da za su abku nan gaba, kuma za su ci gaba da kyautata shirin tafiye-tafiye.

"Ga masu yawon shakatawa dake bukatar shiga taksi, hakan ya sa, za mu amince da taksi masu yawa rika shiga shiyyar. Bisa yawan tikitocin da aka sayar, muna iya ganin cewa, za mu fuskanci kalubale da dama a nan gaba. Za mu kyautata shirye-shiryen tafiye-tafiye don magance kalubalen yawan masu yawon shakatawa."

Yawancin masu yawon shakatawa da suka shiga shiyyar suka so cin abinci iri iri na duniya. Lin Shengyong, shugaban hukumar ba da hidima da kula da harkokin kasuwanci ta shiyyar Expo ya ce, a cikin shiyyar, akwai kamfanoni 100 da suke samar da abinci, kuma an kafa dakunan cin abinci 130. Ana iya samar da abinci iri iri kimanin dubu 300 zuwa dubu 400 a kowace rana. Amma duk da haka, an yi fama da karancin abinci da sauran matsaloli wajen sayar da abinci a cikin shiyyar, amma yanzu komi na zuwa daidai.

"Muna bukatar kamfanonin samar da abinci su kara karfin samarwa, da yawan teburan cin abinci da ma'aikata masu ba da hidima."(Asabe)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China