Cibiyar nuna wasanni ta Bomas ta kasar Kenya dake karkashin shugabancin ministan yawon shakatawa na kasar, ita ce ta dauki nauyin aikin nuna wasanni na kungiyar wakilai ta kasar Kenya a gun wannan biki na EXPO, ita ce kuma kungiyar dake nuna wasanni a game da al'adun kabilu da ta fi girma a kasar Kenya. A ranar da ake shirin yin nune-nune a rumfar kasar Kenya a yayin bikin EXPO, 'yan wasanni 18 na cibiyar za su nuna wasanni, Samson Otieno, da Elizabeth Leigulesei sun kasance daga cikinsu. Yanzu, suna zura ido kan wannan aiki da za su yi a watan Satumba. Samson Otieno ya ce, 'Ina kaunar kasarmu, kuma ina son aikina. Na yi farin ciki sosai, saboda zan wakilci kasarmu don nuna al'adunmu a biki na EXPO. A lokacin kuma, mu da abokai daga kasashe daban daban za mu iya yin koyi da juna, kuma za a kara sada zumunta tsakaninmu.'