Han Qide ya je ofishin jakadan kasar Nijeriya dake kasar Sin don nuna jejeto ga rasuwar tsohon shugaban kasar Nijeriya Yar'Adua
A ran 10 ga wata, Han Qide, mataimakin shugaban kwamitin din-din-din na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya je ofishin jakadan kasar Nijeriya dake kasar Sin, inda a madadin gwamnatin kasar Sin, Han Qihua ya nuna jejeto a game da rasuwar tsohon shugaban kasar Nijeriya Alhajin Umaru Musa Yar'Adua, kuma ya ajiye kambun furanni. A kan littafin nuna jejeto, mista Han Qide ya rubuta cewa, ya nuna alhini ga rasuwar tsohon shugaban kasar. Jakada Bassey U. Eyo, mataimakin shugaban ofishin jakadancin kasar Nijeriya dake kasar Sin ya yi godiya a game da ziyarar. Manyan jami'an ma'aikatar harkokin waje da na ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin su ma sun je ofishin don nuna alhini.(Asabe)