Daga ran 20 ga watan jiya da aka yi gwajin gudanar da bikin EXPO har zuwa ran 9 ga wata, yawan mutane masu yawon shakatawa a rumfar bunkasa rayuwa da farantan ran nakasassu ya riga ya zarce dubu 110, wadanda suka yaba sosai ga rumfar. A kokarin dimbin masu yawon shakatawa na gida da na waje sun fahimci yaddar sha'anin nakasassu na kasar Sin ke bunkasuwa, da kuma rawar da rumfar ke kara takawa, yau litinin wato 10 ga wata, an kaddamar da bikin makon rumfar bunkasa rayuwa da faranta ran nakasassu. Hui Liangyu, mataimakin firayim ministan kasar Sin kuma shugaban kwamitin kula da ayyukan nakasassu na majalisar gudanarwa ta kasar ya sanar da bude makon rumfar. Ya ce, "Yanzu na sanar da cewa, an kaddamar da bikin makon rumfar bunkasa rayuwa da faranta ran nakasassu na bikin EXPO na Shanghai."