in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude bikin makon rumfar rayuwa da rana a taron EXPO na Shanghai
2010-05-10 12:23:40 cri

A ran 10 ga wata, an bude bikin makon rumfar rayuwa da rana da ke dangane da taimakawa nakasassu a taron EXPO na Shanghai. Mataimakin firayim ministan kasar Sin kuma babban darekatan kwamitin kula da harkokin nakasassu na gwamnatin gudanarwa ta kasar Hui Liangyu ya sanar da budewar bikin.

Rumfar rayuwa da rana a taron EXPO na Shanghai ta kasance rumfa ta farko da ke dangane da nakasassu na tarihin bikin EXPO wadda ya shafe shekaru 159.

A gun taron budewar bikin, shugabar hadaddiyar kwamitin kula da harkokin nakasassu na kaasr Sin Zhang Haidi ta bayyana cewa, a gun bikin EXPO za a iya gano al'adu da fasahohi na iri daban daban na duniya, ba ma kawai bikin EXPO ya kawo tasiri mai kyau ga birane da zaman rayuwa ba, har ma ya kawo fatan mai kyau ga nakasassu.

Tun daga ran 20 ga watan jiya zuwa ran 9 ga wata, yawan mutanen da suka ziyarci rumfar rayuwa da rana a taron EXPO na Shanghai ya wuce dubu 110.(Abubakar)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China