in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta zama abin koyi a kasashe masu tasowa
2010-05-07 14:30:31 cri

Ran 7 ga wata ita ce ranar rumfar kasar Sierra Leone na bikin EXPO na birnin Shanghai, kuma ita ce rana ta farko ta rumfar kasashen Afirka.

A ran nan, shugaban rumfar kasar Sierra Leone na bikin EXPO a birnin Shanghai Sumanu Othman Zinurine Alghali ya bayyana cewa, kasar Sin ta ci nasara wajen gudanar da bikin EXPO, wannan ya zama abin koyi ga kasashe masu tasowa, kuma wannan ya shaida cewar kasashe masu tasowa sun iya gudanar da bikin koli na kasa da kasa.

A matsayin sabon shugaban hadaddiyar rumfar kasashen Afirka, Sumanu Othman Zinurine Alghali ya bayyana cewa, zai tattauna kan hanyar jawo hankali jama'ar kasar Sin tare da sauran masu shirya rumfar kasashen Afirka.

Ban da haka kuma, Sumanu Othman Zinurine Alghali ya bayyana cewa, burin da ya sa kasar Sirea Leone ta shiga bikin EXPO shi ne nuna al'adun kasar da sa kaimi ga yin hadin gwiwa tare da kungiyoyi da mutane masu zaman kansu da bayyana wa masu zuba jari babban boyayyen karfi a fannin bunkasuwar kasar don samu jarin kasashen waje.(Abubakar)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China