in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-Moon ya nuna juyayi game da rasuwar tsohon shugaban kasar Nijeriya Umaru Yar'Adua
2010-05-07 09:10:37 cri

A ran 5 ga wata dare, babban sakataren M.D.D Ban Ki-Moon ya bayar da sanarwa, inda ya nuna juyayi game da rasuwar tsohon shugaban kasar Nijeriya Umaru Yar'Adua, kuma ta bayyana cewa, rasuwarsa ya kawo babban hasara ga gwamnati da jama'ar kasar Nijeriya.

A cikin sanarwar, Ban Ki-Moon ya nuna godiya ga goyon bayan da Umaru Yar'Adua ya nuna wa M.D.D a yayin da yake shugaban kasar Nijeriya, kuma Ban Ki-Moon ya nuna godiya ga aikin da Umaru Yar'Adua ya yi a yayin da ya rike shugabancin karba-karba na kungiyar ECOWAS. A sa'i daya kuma, Ban Ki-Moon ya nuna jejeto ga iyalin Umaru Yar'Adua da gwamnatin kasar Nijeriya.

A ran 5 ga wata da dare, a Abuja, babban birnin kasar Nijeriya, Allah ya yi wa shugaban kasar Najeriya Alhaji Umaru Yar'Adua rasuwa. A ran 6 ga wata, Goodluck Jonathan ya yi rantsuwar zama shugaban kasar Nijeriya.(Abubakar)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China