in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya nuna alhini ga rasuwar marigayi shugaba Umaru Yar'Adua na Nijeriya
2010-05-06 22:32:41 cri
A ran 6 ga wata, Mr. Hu Jintao, shugaban kasar Sin ya aika wa shugaban kasar Nijeriya na yanzu Jonathan Goodluck sako, inda Mr. Hu ya wakilci gwamnati da jama'ar kasar Sin da sunansa yan nuna alhini sosai ga rasuwar shugaba Umaru Yar'Adua, kuma ya nuna janjantawa gwamnati da jama'ar kasar Nijeriya da iyalin Umaru Yar'Adua.

A cikin sakonsa, Mr. Hu ya ce, marigayi shugaba Umaru Yar'Adua gaggan shugaba ne na kasar Nijeriya. Lokacin da yake raye, ya mai da hankali sosai wajen neman ci gaban kasarsa da al'ummominsa. Shi kuma amini ne na jama'ar kasar Sin, ya kan tsaya tsayin daka kan matsayin sada zumunci a tsakanin kasashen Sin da Nijeriya, har ma ya bayar da muhimmiyar gudummawa wajen kokarin kafa huldar abokantaka tsakanin kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare. Muna fatan Allah ya jikansa.

Mr. Hu ya kara da cewa, gwamnatin kasar Sin tana mai da hankali sosai kan dadaddiyar huldar da ke kasancewa a tsakanin kasashen Sin da Nijeriya, kuma tana son yin kokari tare da gwamnatin kasar Nijeriya domin ci gaba da bunkasa huldar abokantaka a tsakanin kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China