in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
(Sabunta)Goodluck Jonathan ya yi rantsuwar kama mukamin shugabancin kasar Nijeriya
2010-05-06 19:07:35 cri

A ranar 6 ga wata a Abuja, babban birnin kasar Nijeriya, mukaddashin shugaban kasar, Goodluck Jonathan ya yi rantsuwar kama mukamin shugabancin kasar.

A yayin da yake yin jawabi ta talibijin a fadar shugaban kasa, Mr. Jonathan ya nuna babban alhini ga rasuwar shugaba Umaru Musa Yar'Adua. A waje guda kuma, ya yi alkawarin cewa, kafin zaben shugaban kasar da za a shirya a shekara mai zuwa, zai yi kokari da nufin gudanar da harkokin siyasa masu kyau a kasar Nijeriya, kuma zai mayar da hankali kan aikin gyare-gyaren tsarin zabe.

Jonathan ya kara bayyana cewa, babbar matsalar da gwamnatin kasar Nijeriya ke fuskanta a yanzu ita ce, ko kowa da kowa a kasar Nijeriya zai iya shiga zaben, ko a'a. Dadin dadawa, Jonathan ya yi alkawarin cewa, za a kara gudanar da ayyukan hana cin hanci da rashawa, gami da tabbatar da zaman lafiya a yankin Niger Delta mai arzikin man fetur da ke kudancin kasar. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China