in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Allah ya yi ma shugaban Najeriya Alhaji Umaru Musa Yar'Adua rasuwa
2010-05-06 16:40:20 cri

Ran 5 ga wata da dare, kakakin shugaban kasar Najeriya ya sanar wa kafofin watsa labaru cewa, shugaban Najeriya Alhaji Umaru Musa Yar'Adua da ya shafe tsawon lokaci yana fama da rashin lafiya ya rasu a daren wannan rana da karfe 9 da rabi a fadar shugaban kasar da ke birnin Abuja, hedkwatar kasar. Shekarunsa 58 ne kawai a duniya. Goodluck Jonathan, mukaddashin shugaban kasar an rantsar da shi a matsayin shugaban kasar a ran 6 ga wata da karfe 8 na safe.

Fadar shugaban Najeriya ta sanar da cewa, za a gudunar da jana'izzar Yar'Adua a garinsa wato jihar Katsina da ke arewacin kasar a ran 6 ga wata da yamma. Kuma tun daga ran 6 ga wata, za a yi zaman makoki a duk kasar har na tsawon kwanaki 7, tare da saukar da tutar kasa zuwa rabin sanda domin nuna juyayin rasuwar shugaba Yar'Adua.

Yar'Adua ya zama shugaban Najeriya a shekarar 2007. Kokarin da ya yi ya ba shi damar samun amincewa daga jama'a da akasarin ra'ayoyin jama'a, amma ya dade yana shan aiki, abin da ya jawo masa rashin isasar lafiya. A ran 23 ga watan Nuwamba na shekarar bara, an je ba shi wata likita a kasar Saudiya saboda matsalar zuciya. Bayan haka kuma, ya kwanta, rashin lafiya abun da ya hana shi a fili, duk da bai mika ikon kasa ga hannun mataimakinsa ba. Ta haka Najeriya ta yi watanni da dama ba ta da shugaba. Duk da haka a watan Feburairu na bana, mataimakin shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya zama mukaddashin shugaban kasar, kuma Yar'Adua ya koma gida daga Saudiya, amma ya ci gaba da jiyya a fadar shugaban kasar. A watan jiya, Jonathan ya kafa sabuwar majalisar ministocin kasar, an samu kwanciyar hankali a Najeriya.

Najeriya, kasar Afirka ce mafi yawan mutane, kuma mafi arzikin man fetur. Duk da haka 'yan tawayen Nijer Delta su kan kawo cikas wajen samar da man fetur a wannan kasa. Gwamnatin Najeriya tana fatan ta hanyar yafe wa 'yan tawayen Nijer Delta ne za a samu zaman lafiya a wurin da kuma tabbatar da samar da man fetur. Amma an dakatar da dukkan shawarwari dalilin tafiyar Yar'Adua a Saudiya. Tun daga watan Disamba na bara, 'yan tawaye sun sha kai hare-hare kan bututun man fetur sau da dama, ta haka sauyin halin da Najeriya ke ciki a harkokin siyasa ya zama daya daga cikin dalilan da suka sauya farashin man fetur a kasuwannin duniya.

A watan Maris na bana, kwamitin kula da harkokin zabe na Najeriya mai zaman kansa ya sanar da cewa, za a gudanar da zaben shugaban kasar a ran 22 ga watan Janairu ko kuma ran 23 ga watan Afrilu na shekara mai zuwa. Wasu manazarta na Najeriya suna ganin cewa, bayan rasuwar Yar'Adua, za a sassauta halin kaka-ni-ka-yi a tsakanin jam'iyyu da ma rukunonin siyasa daban daban a Najeriya, ta haka za a dan rage cikas da gwamnatin wucin gadi da ke karkashin shugabancin Jonathan ke fuskanta. Amma wasu na ganin cewa, a Najeriya, ana bin wata al'adar gargajiya da ba a rubuta cikin doka ba a fagen siyasa, wato a kan yi musayar ikon shugabantar kasar a tsakanin wanda ya fito daga kudancin kasar da kuma wanda ya fito daga arewacin kasar a ko wadanne shekaru 8. Yar'Adua, wani Bahaushe ne daga jihar Katsina a arewacin Najeriya, kuma wani musulmi ne. Jonathan kuma, wani dan Ijaw ne daga jihar Bayelsa a kudancin kasar, yana bin addinin Kirista. A shekarar 2007, Yar'Adua ya karbi ragamar mulkin kasa daga hannun Olusegun Obasanjo da ya fito daga kudancin kasar. Ya zuwa yanzu shekaru 2 ko fiye kawai sun wuce. Idan a daidai wannan lokaci, Jonathan da ya fito daga kudancin Najeriya ya hau karagar mulkin kasa, to, mai yiwuwa ne a ganin mazauna arewacin kasar, Jonathan bai bi al'adar gargajiya da ake saba bi a harkokin siyasa a Najeriya ba. Sakamakon haka, ana bukatar ci gaba da sa ido kan halin da ake ciki a Najeriya a fagen siyasa. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China