A ran 5 ga wata, Allah ya yi wa shugaban kasar Nijeriya Alhaji Umaru Yar'Adua rasuwa. A ran 6 ga wata, a birnin Beijing, Jiang Yu, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ta bayyana cewa, kasar Sin ta nuna Alhini a game da rasuwar shugaban kasar Nijeriya wadda ya rasu sakamakon dogon rashin lafiya, kuma tana fatan ci gaba da yin kokari tare da kasar Nijeriya don bunkasa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare yadda ya kamata.
Yar'Adua ya kai ziyara ga kasar Sin a shekarar 2006
Madam Jiang Yu ta bayyana haka ne yayin da take amsa tambayoyin manema labaru a gun taron manema labaru da ma'aikatar harkokin waje ta saba yi. Jiang Yu ta furta cewa, muna nuna alhini a game da rasuwar shugaban kasar Nijeriya Alhaji Umaru Yar'Adua, kuma muna nuna jajantawa ga iyalan shugaban da gwamnatin kasar da kuma jama'ar kasar. Alhaji Umaru Yar'Adua ya ba da gudummawa sosai wajen bunkasa kasar Nijeriya da dangantakar dake tsakanin Sin da Nijeriya. Muna fatan yin kokari tare da Nijeriya don ci gaba da bunkasa dangantakar abokantaka dake tsakanin kasashen biyu.(Asabe)