in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana gudanar da bikin EXPO na Shanghai bisa ka'idar "rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli"
2010-05-05 20:27:09 cri

Ran 5 ga wata, Mr. Zhang Quan shugaban hukumar kiyaye muhalli ta birnin Shanghai da ke gabashin kasar Sin ya nuna cewa, a lokacin da ake shirya bikin baje koli na duniya (EXPO) na Shanghai, har ma da ake gudanar da bikin yanzu, ko da yaushe ana bin ka'idar "rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli".

A gun taron manema labaru da aka yi a bikin EXPO na Shanghai, Mr. Zhang Quan ya bayyana cewa, kafin fara shirya bikin EXPO, an zabi wurin gina farfajiyar bikin EXPO a unguwa ta zamanin da, an rufe tare da sake gidajen kamfannoni masu gurbata muhalli 272, kuma yayin da ake gina farfajiyar bikin EXPO, an yi amfani da fasahohin yin tsimin makamashi da ruwa, da makamashin hasken rana da dai sauransu. A lokacin da ake gudanar da bikin EXPO yanzu, ana amfani da motocin bas-bas fiye da dubu daya da ke amfani da makamashi maras gurbata muhalli a farfajiyar bikin EXPO.

Babban taken bikin EXPO na Shanghai shi ne "birni mai kayatarwa, da rayuwa mai inganci", kuma dakuna da abubuwan da ake nunawa a farfajiyar bikin suna bin ka'idar "rage fitar da abubuwa masu gurbatawa da kiyaye muhalli, da neman bunkasuwa mai dorewa, da zaman rayuwa mai dacewa." [Musa Guo]

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China