in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masu yawon shakatawa na kasashen waje za su ji dadin ziyartar bikin Expo na Shanghai
2010-05-04 16:42:59 cri

A ranar 4 ga wata, an shiga mataki na sayar da tikiti ga kowa da kowa a gun bikin baje-koli na duniya na shekara ta 2010 da ake yi a birnin Shanghai, masu yawon shakatawa na iya sayen tikiti a bakin kofar farfajiyar bikin Expo, domin shiga ciki kai tsaye. Ya zuwa karfe 2 da yamma a wannan rana, masu yawon shakatawa kimanin dubu 130 sun shiga cikin farfajiyar bikin Expo, kuma wannan adadi ya tasar wa yawan mutanen da suka ziyarci bikin Expo a ranar 3 ga wata. An kimanta cewa, bikin Expo zai jawo hankalin masu yawon shakatawa na kasashen waje kimanin miliyan 3.5, kuma za su ji dadin ziyartar bikin Expo na Shanghai.

Masu yawon shakatawa na kasashen waje sun bayyana cewa, suna sha'awar rumfuna masu kayatarwa kimanin 100, cikinsu, za su kai ziyara a rumfar kasar Sin da rumfunan kasashensu da rumfunan kasashen Turai da Amurka, kana masu yawon shakatawa na kasashen waje sun nuna sha'awa sosai game da wasannin da ake yi a cikin farfajiyar bikin Expo. A ko wace rana, a kan nuna wasannin da ke shafar al'adu kimanin 100, kuma a kan yi faretin motocin da aka yi wa adon furanni har na tsawon awoyi 5. Masu yawon shakatawa sun bayyana cewa, an nuna al'adu na kasashe daban daban da tunani samar da abubuwa masu kayatarwa a gun bikin Expo.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China