in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bikin baje koli na duniya na Shanghai shi ne wani gagarumin shagali ga kasa da kasa wajen yin mu'amalar juna
2010-05-04 15:32:16 cri
A ran 2 ga wata, yayin da yake hira da wakilinmu, Moses Wetangula, ministan harkokin waje na kasar Kenya wanda ya zo kasar Sin don halartar bikin bude bikin baje koli na duniya na Shanghai a shekarar 2010 ya nuna babban yabo ga bikin baje koli na duniya na Shanghai, kuma ya ce bikin wani gagarumin shagali ne ga kasa da kasa wajen yin mu'amala da juna. Ya bayyana cewa, a matsayinta na kasa mai tasowa, kasar Kenya na shiga bikin baje koli na duniya a wannan karo domin ta koyi abubuwa daban daban daga kasa da kasa, a sa'i daya kuma, tana fatan yin musayar ra'ayi kan nasarar da ta samu wajen kiyaye muhalli da dai sauransu.

Mista Wetangula ya nuna babban yabo ga taken bikin baje koli na duniya na Shanghai wato 'Birni mai kayatarwa da rayuwa mai inganci'. A ganinsa, a gun bikin baje koli na duniya, ana jaddada cewa, dole ne a yi amfani da kimiyya da fasaha don ba da himma ga dan Adam.

"Akwai bambanci a tsakanin bikin baje koli na duniya a wannan karo da wadanda aka yi a baya. A gun bikin a wannan karo, ana jaddada yin amfani da kimiyya da fasaha don kyautata zaman rayuwar dan Adam. Wannan shi ne dalilin da ya sa aka tsara babban taken bikin 'Birni mai kayatarwa da rayuwa mai inganci'. Mutanen da suka halarci bikin baje koli na duniya na Shanghai za su koyi abubuwa da dama, kuma abin da suka koya zai taimaka wajen ba da himma ga mutane na duk fadin duniya da kyautata zaman rayuwarsu. Ina ganin cewa, kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban bikin baje koli na duniya. An shirya bikin baje koli na duniya na Shanghai yadda ya kamata, hakan ya zama abin koyi ga kasa da kasa."

Mista Wetangula yana mai ra'ayin cewa, bikin baje koli na duniya na Shanghai wani gagarumin shagali ne ga kasa da kasa ta yadda za su taru waje guda don koyi da juna.

"Mun zo bikin don mu yi koyi daga kasa da kasa. A gun bikin, za mu yi mu'amala da masu zuba jari, kuma za mu halarci bikin nune-nune na kasashe daban. Bayan da muka koya wasu muhimman abubuwa daga sauran kasashe, za mu yi watsi da abubuwa marasa kyau, mu kuma ci gaba da ayyukan dake dacewa da halin da muke ciki yayin da muke samun ci gaba a nan gaba."

Ban da haka kuma, mista Wetangula ya darajanta dangantakar dake tsakanin Sin da Kenya da huldar dake tsakanin Sin da Afrika. Ya furta cewa, lokacin da kasashen Afrika suke yunkurin samun mulkin kai da neman samun bunkasuwa, kasar Sin ta kan nuna goyon baya gare su. Kasar Sin ita ce abokiyar kasashen Afrika da ake iya amince da ita.

"Afrika nahiya ce dake samun babban ci gaba. Yayin da ake samun ci gaba a nahiyar Afrika, kasar Sin ta kan tsaya tare da Afrika. Kasar Sin ita ce abokiyar nahiyar Afrika mai daidaici, ba ta je Afrika don kwace dukiya ba, amma ta je Afrika don bunkasa nahiyar. Daga kasar Kenya har zuwa duk fadin nahiyar Afrika suna ganin cewa, hadin gwiwa mai daidaici dake tsakanin Sin da Afrika zai bunkasa bangarorin biyu. Ba kawai hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afrika zai jawo moriya ga Kenya da sauran kasashen Afrika ba, hatta ma zai jawo moriya ga dukkan kasashen duniya."(Asabe)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China