Shugaba Hu Jintao ya kuma tabbatar da cewa, hakika zasu samar da ingantacciyar kariya tare da gudanar da ayyuka masu inganci wanda hakan zai bada daman samun nasarar gudanar da bikin baje kolin kayayyaki na duniya wato Expo a cikin nasara.Ya kara da cewa biki ne da ba za a taba mantawa da shi ba .
Sauran wadanda suka halarci bikin sun hada da Jia Qinglin da Li Changchun da Xi Jinping da He Guoqiang da Zho Yonkang.
Bikin da za a shafe watanni shida ana gudanarwa za a kammala a ranar 31 ga watan Oktoba na wannan shekara kuma ana sa ran bikin zai samu halartan jama'a kimanin miliyan saba'i.(AbdulAziz Mu'azu)