Mohammed Dirir, ministan al'adu da yawon shakatawa na kasar Habasha ya bayyana cewa, a wajen bude bikin EXPO na Shanghai, an hada da wasanni masu kayatarwa da wasan wuta tare, wanda ya burge mutane sosai. Kasar Sin ta sake nuna kwarewarta a gaban duniya ta fuskar shirya gagarumin biki da kuma hadin kan Sinawa.
Raphel Hawklolo, wani jami'in ma'aikatar watsa labarai da al'adu da wasanni ta kasar Tanzania ya furta cewa, bikin EXPO na samar da wata kyakkyawar dama wajen kara cudanyar da ke tsakanin kasa da kasa da kuma kara fahimtar juna, wanda kuma zai sa kaimi ga bunkasuwar dangantakar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka kana da sauran kasashe masu tasowa.(Kande Gao)