Bayan da ta kalli bikin kaddamar da EXPO, shugabar kungiyar hadin-gwiwar Sinawa dake kasar Amurka Madam He Xiaohui ta bayyana cewa, wannan biki yana da kayatarwa sosai, wanda ya hada salon musamman na kasar Sin da sauran abubuwa iri-iri a duniya da kyau, lamarin da ya bayyana kyakkyawan fata na jama'ar kasar Sin na shimfida zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya baki daya.
A nasu bangaren kuma, Sinawa dake kasar Jamus sun yi tattaunawa tare da farin-ciki a kan bikin kaddamar da EXPO. Haka kuma babban edita na Jaridar Europe Daily News, wadda ta kasance jarida mafi girma da ake bugawa da harshen Sinanci a Jamus, Fan Xuan ya ce, kaddamar da bikin EXPO a Shangahi ba ma kawai zai inganta mu'amala dake tsakanin kasar Sin da duniya baki daya ba, har ma dukkan mutanen duniya zasu kara fahimtar yadda kasar Sin take.
Dadin dadawa kuma, a nasa bangare, wani memban rukunin likitoci na kungiyar wanzar da zaman lafiya da kasar Sin ta tura zuwa kasar Kongo(Kinshasa) Guo Yunfei ya ce, gagarumin bikin bude EXPO da aka shirya ya nuna babban karfi na kasar Sin.(Murtala)