in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hu Jintao ya shirya liyafa domin maraba da gaggan baki masu halartar taron bude bikin baje koli na duniya na Shanghai
2010-04-30 20:20:06 cri

A ran 30 ga wata da dare, a madadin gwamnati da jama'ar kasar Sin, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya shirya liyafa domin maraba da gaggan baki masu halartar taron bude bikin baje koli na kasa da kasa na shekarar 2010. Hu Jintao ya bayyana cewa, bikin baje koli na duniya na Shanghai shi ne a karo na farko da aka shirya bikin baje koli na duniya a wata kasa mai tasowa. Bikin ya zama wata dama ga kasar Sin kuma ya zama wata dama ga kasa da kasa. Jama'ar kasashen duniya za su iya jin dadi a gun bikin baje koli na duniya na Shanghai.

A yayin liyafar, Hu Jintao ya yi jawabi mai taken "taruwa a bikin baje koli na kasa da kasa da kuma samar da kyakkyawar makoma". Inda Hu Jintao ya bayyana cewa, ta hanyar bikin baje koli na duniya na Shanghai za a nunawa kasashen duniya game da kasar Sin wadda ke gudanar da manufar bude kofa ga kasashen ketare da yin gyare-gyare da samun bunkasa sosai, kuma ta hanyar bikin za a kafa wata gadar yin hadin gwiwa da koyi da juna. Bikin baje koli na duniya na Shanghai zai daga matsayin koyi da juna da ke tsakanin jama'ar kasar Sin da na kasa da kasa da daga matsayin koyi da juna da ke tsakanin al'adu daban daban na duniya.(Abubakar)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China