in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sabunta: Shugaban kasar Sin ya yi maraba da gaggan baki masu halartar taron bude bikin baje koli na duniya na Shanghai
2010-04-30 19:34:36 cri

Ran 30 ga wata da dare, a birnin Shanghai, shugaba Hu Jintao na kasar Sin da kuma uwar gidansa Liu Yongqing sun shirya liyafa domin maraba da gaggan bakin da za su halarci taron bude bikin baje koli na kasa da kasa na shekarar 2010.

Gaggan baki fiye da 40 sun halarci liyafar, ciki har da shugaba Denis Sassou Nguesso na kasar Kongo(Brazzaville), da Kim Yong Nam, shugaban zaunannen kwamitin majalisar jama'ar kasar Korea ta Arewa, da shugaba Nicolas Sarkozy na kasar Faransa da uwar gidansa, da shugaba Ali Bongo na kasar Gabon da uwar gidansa, da shugaban kasar Pakistan kuma shugaban hukumar ikon al'ummar kasar Mahmoud Abbas, da shugaba Lee Myong-Bak na kasar Korea ta Kudu da uwar gidansa, da firayim minista Hun Sen na kasar Cambodia da uwar gidansa, da shugaba Jose Manuel Barroso na kwamitin kungiyar tarayyar Turai, da shugaba Jean-Pierre Lafon na hukumar kula da harkokin nune-nune ta kasa da kasa da dai sauransu.

A yayin liyafar, shugaba Hu ya yi jawabi mai taken "taruwa a bikin baje koli na kasa da kasa da kuma samar da kyakkyawar makoma".(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China